An kashe masu ikirarin jihadi 20 a Mali

Dakarun Faransa 4,500 ne ke fafutikar kakkabe mayaka a yankin Sahel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Faransa 4,500 ne ke fafutikar kakkabe mayaka a yankin Sahel

Kasar Faransa ta ce dakarunta dake arewacin Mali sun kashe masu ikirarin jihadi 20 a wannan makon.

Ma'aikatar tsaro ta ce an yi amfani jiragen yaki da wasu masu saukar angulu a farmakin da dakarun Faransan suka kai.

Faransa dai tana da dakaru dubu hudu da dari biyar dake fafutikar kakkabe mayakan a yankin Sahel.

An dai raunata sojojin Faransa hudu a wani harin roka da aka kai ranar Alhamis kwana guda bayan da aka kashe wasu sojojin Mali uku a wata arangama da suka yi da mayakan.