Theresa May da Jeremy Corbyn sun sha tambayoyi a muhawara

UK Election
Image caption Theresa May da Jeremy Corbyn sun sha tambayoyi masu zafi daga masu kada kuri'a a zauren muhawara

Firai Ministan Burtaniya, Theresa May, da jagoran babbar jam'iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn, na fuskantar tambayoyi daga masu kada kuri'a a muhawarar karshe ta gidan talbijin kafin babban zaben kasar da za'a gudanar mako mai zuwa.

Wadanda suka halarci zauren muhawara sun yi musu tambayoyi a lokuta daban daban bayan da Mrs May ta ki amince wa a tafka muhawara gaba da gaba da shugabannin sauran jam'iyu.

Ta jaddada cewa ita ce ta fi dacewa ta jagoranci tattaunar ficewar kasar daga tarayyar turai, yayin da kuma ta sha tambayoyi masu zafi daga masu kada kuri'a game da batun tsuke bakin ajihu.

Anasa bangaren Mr Corbyn ya yi alkawarin cewa manufofin jam'iyyar su kan tsuke bakin aljihu sun fi dacewa da kasar, inda aka kalubalance shi game da tarin basussuka da gwamnatin jam'iyyar Labour data shude ta bari.

Labarai masu alaka