Malaysia ta sa kyautar kudi ga bidiyon da ya nuna illar luwadi

Malaysia gay Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane 'yan luwadi na gamuwa da hukunci a Malaysia.

Hukumomi a Malaysia sun kare matakin da suka dauka, na sanya kyautar kudi dala dubu daya, ga wasu bidiyoyi da suka nuna yadda mutane za su iya kaucewa luwadi.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce ba an shirya gasar ba ce don a nuna wariya ga wata kungiya, amma an yi hakan ne domin a taimakawa matasa daukan matakin da ya dace game da lafiyarsu.

Hukumomi a kasar sun bukaci mutane da su mika bidiyoyi da suke nuna illolin mutun ya kasance dan luwadi, ko kuma yin wasu dabi'u na jinsin da ba nashi ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kakkausan suka ga gasar.

Mutane 'yan luwadi na gamuwa da hukunci a Malaysia.