Real Madrid ta lashe gasar zakarun Turai

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Real Mardid sun yi ta murna bayan sun dauki kofin gasar zakarun turai

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar zakarun Turai bayan ta doke Juventus da 4-1 a wasan karshen da suka buga a birnin Cardiff da ke Birtaniya.

Christiano Ronaldo ya sha wa Real Mardid Kwallo ta farko minti 20 da fara wasa, amman Mario Mandzukic ya dau wa Juventus fansa bayan minti bakwai (minti 27 da fara wasa).

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallo na biyun da Christiano Ronaldo ya sha kenan minti 64 da fara wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Carlos Casemiro ya zura wa Real Madrid kwallo ta biyu a ragar Juventus minti 61 da fara wasa, kuma Christiano Ronaldo ya kara wa Juventus bayan minti uku (minti 64 da fara wasa).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya lashe gasar zakarun turai sau hudu, uku da Real Madrid, daya da Manchester United

Juan Cuadrado da ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci ya samu jan kati minti 84 da fara wasa lamarin da ya rage 'yan wasan Juventus da ke kan fili daga 11 zuwa 10.

Duk da haka Real Madrid ba ta kyale Juventus ba domin Marco Asensio ya kara mata kwallo daya minti 90 da fara wasa abin da ya sa aka tashi wasan 4-1.

Hakkin mallakar hoto EPA/ AFP AND GETTY IMAGES
Image caption Kwallo mai kayatarwar da Mario Mandzukic ya sha wa Juventus ta babbaya ya kasa kare Juve daga shan kaye

Labarai masu alaka