Nigeria ta yi tir da janyewar Amurka daga yarjejeniyar Paris

Shugaba Muhammadu Buhari na da burin mutunta yarjejeniyar Paris Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari na da burin mutunta yarjejeniyar Paris

Gwamnatin Nigeria ta bayyana takaicinta akan shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka ta janye kasar daga yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a Paris.

A wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce yarjejeniyar Paris da aka cimma, an yi da nufin ci gaban daukacin bil'adama da kuma duniya baki daya.

Sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Clement Onoja Aduku ya sanya wa hannu, ta ce Nigeria, kamar sauran kasashen duniya da suka rattaba hannu a yarjejeniyar, za ta ci gaba aiwatar da nata alkawarin karkashin yarjejeniyar kamar dai yadda burin shugaban kasar yake wajen ganin an mutunta yarjejeniyar.

Tun bayan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya fitar ranar Alhamis, kasashen duniya da dama dai suka yi ta Allah-wadai game da matakin ficewar Amurka daga yarjejeniyar.

Firayim Ministar Birtaniya,Theresa May ta shaida wa Shugaba Donad Trump takaicinta kan shawarar ficewa daga yarjejeniyar.

Wata sanarwar da fadar Downing Street ta fitar, ta ce a tattaunawar ta da shugaba Trump ta wayar tarho, Firayim ministar Burtaniyar ta ce yarjejeniyar Paris din ce ta ba da tsarin duniya na kare ci gaba da kuma tsaron karni na gaba baya ga samar da makamashi mai rahusa ga mutane da kuma kamfanoni.

Kungiyar tarayyar Turai ta ce ranar Alhamis wata rana ce ta bakin ciki ga duniya, sai dai za ta ci gaba da yakar dumamar yanayi domin tarihi na bayanta.

Shima a nasa martanin, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce Faransa ba za ta sake wata sabuwar tattaunawa domin samun yarjejeniya mai karamar manufa ba ko ta yaya.

Duk da cewar kungiyar da ke rajin kare hakkin masu makamashin kwal a Amurka ta yi maraba da matakin shugaba Trump din, gwamnonin jihohin Washington da New York da kuma Carlifornia tare da magadan gari a biranen Amurka 61 sun yi tir da matakin da shugaban ya dauka, kuma sun lashi takwobin yakar dumamar yanayi.

Sai dai kuma babu tabbacin irin tasirin gwamnoni da kuma magadan garin za su yi kan dumamar yanayi.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Masana dai sun yi gargadin cewa duniya na fuskantar barazana kan dumamar yanayi

A shekarar 2015 ne dai shugabannin kasashen duniya da wakilai daga kasashe 195 da suka halarci taron koli kan sauyin yanayi a Paris suka amince da yadda za a rage dumamar duniya bayan tsawon shekaru hudu ana muhawara a kan batun.

Labarai masu alaka