Ba zan daka ta Trump ba – Sadiq Khan

Sadiq Khan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sadiq Khan ne Musulmi na farko da ya zama Magajin Garin Landan a shekarar 2016

Magajin Garin Landan Sadiq Khan ya ce ba shi da lokacin tankawa Shugaban Amurka Donald Trump game kalaman da ya danganta shi da su a shafinsa na Twitter, bayan harin da aka kai birnin Landan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Magajin Garin Ladan Sadiq Khan kan kalamansa da ya yi game da harin birnin Landan ranar Lahadi da safe.

Mista Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Akalla mutum bakwai ne suka mutu wasu kuma 48 suka jikkata. Magajin Garin Landan ya ce 'babu dalilin da za mu sanya kanmu a damuwa'," inji Trump.

Shugaban yana alakanta maganar da Mista Khan ya yi ranar Lahadi da safe ne, inda ya ce yana alhini da wadanda harin Landan ya shafa kuma ya ce masu tada kayar bayan "ba za su yi nasara ba"

Magajin garin ya ci gaba da cewa "Mazauna Landan za su ga karuwar jami'an tsaro a yau da kuma kwanaki masu zuwa. Babu dalilin da za mu sanyawa kansu damuwa."

Daga nan ya yi Allah-wadai da harin kuma ya bukaci mutane da su kasance masu kula da sanya ido.

Ƙarshen wannan kalaman ne Mista Trump ya dauka ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter.

Sai dai mai magana da yawun Mista Khan ya mayar da martani ga Trump, inda ya ce: "Magajin gari ba shi da lokacin tankawa Trump saboda ya dukufa yana aiki da 'yan sanda da jami'an tsaro bayan harin birnin Landan don samar da shugabancin da ya dace."

Ya ci gaba da cewa "Akwai muhimman al'amura da suke gaban magajin garin kuma ba shi da lokacin tankawa kalaman Trump, wanda ya yi wa sanarwar magajin garin mummunar fahimta wato sanarwar da ke magana kan yadda mazauna garin Landan za su ga karin tsaro a titunan birnin."

A shekarar 2016 ne, Sadiq Khan ya zama Musulmi magajin garin Landan na farko a tarihin birnin.