An tura ƙarin jami'an tsaro masu makamai sassan London

London Bridge
Bayanan hoto,

Wakiliyar BBC Holly Jones, da ke kan gadar, ta ce mai yiwuwa motar da aka kai harin da ita "tana gudun kilomita 50 ne a sa'a guda" inda ta buge "mutum biyar ko shida".

'Yan sanda a Burtaniya sun ce an tura ƙarin jami'ai ɗauke da makamai sassan birnin London, yayin da ake ci gaba da bincike kan harin daren Asabar da ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai, wasu kimanin hamsin suka jikkata.

An kafa sabbin shingayen tsaro cikin dare a wasu gadodji da ke tsakiyar birnin.

'Yan sanda sun gudanar da ƙarin bincike kan wuri biyu a gabashin London, inda ake ci gaba da tsare wasu mutanen, baya ga wasu 11 da tun farko suke hannu.

Ƙungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci ta yi iƙirarin kai harin na birnin London na daren Asabar.

Kafar yaɗa labaran 'yan ta-da-ƙayar-bayan, Amaq, a manhajar aika saƙwanni ta Telegram, ta ce "wani reshen tsaro na mayaƙan ƙungiyar IS ya kai hare-hare a London cikin daren jiya".

A lokaci guda kuma kafofin yaɗa labarai sun bayyana sunan wata 'yar ƙasar Kanada, Christine Archibald a matsayin ɗaya daga cikin mutum bakwai da aka kashe sakamakon hare-haren na daren Asabar.

Danginta sun fitar da wata taƙaitacciyar sanarwa ga gidan talbijin ɗin Kanada CTV, suna cewa ta yi aiki a wani gidan marayu kafin ta koma Turai don ci gaba da zama da wani saurayi da za ta aura.

Rundunar 'yan sandan London ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce nan gaba kaɗan za ta sanar da sunayen mutanen da ake zargi.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Mark Rowley ya ce: "Zan so na tabbatar wa al'umma cewa hakan kai tsaye (rashin bayyana sunayen wadanda ake zargi) na taimaka wa ci gaban binciken, kuma zamu fitar da bayanan mutum uku da kai tsaye suke da hannu wajen kai waɗannan hare-haren."

"Jami'ai na aiki ba dare ba rana don rairaye wuraren da aka aikata laifi" tare da fatan cewa za a sake buɗe wasu yankuna na Gadar London da safiyar Litinin.