'Ana iya sake dakatar da alƙalan da aka mayar aiki'

Court of law
Bayanan hoto,

Sama da wata takwas bayan kai sumame gidajen alƙalan amma ɓangaren zartarwa bai iya gurfanar da dukkansu a kotu ba.

Wani lauya a Nijeriya, Barista Sanusi Musa ya ce tun farko da an yi wa alƙalan da mahukunta suka mayar bakin aiki a baya-bayan nan ritaya maimakon dakatar da su.

A cewarsa wannan na ɗaya daga cikin zaɓin da hukumomi ke da shi a kan alƙali takwas da aka dakatar bisa zarge-zargen da suka haɗar da cin hanci da rashawa.

A ranar Asanar 8 ga watan Oktoban bara, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya ta fitar da wata sanarwa game da wani sumame da jami'anta suka ƙaddamar a gidajen alƙalan da ta zarga.

Ta ce ta gano maƙudan kuɗi a gidajen waɗannan alƙalai da ke jihohi daban-daban a Nijeriya.

Jami'an hukumar kai sumamen ne a babban birnin ƙasar, Abuja da Fatakwal da Gombe da Kano da Enugu da kuma Sakkwato.

Mai magana da yawun hukumar ta DSS, Abdullahi Garba, ya ce an samu kuɗaɗen ƙasashen waje da na gida, yayin sumamen.

Alƙalan da aka kai wa samame sun haɗa da na Kotun koli da na Kotun Ɗaukaka Ƙara da kuma na Manyan Kotunan ƙasar.

Baya ga waɗancan kuɗaɗe da DSS ta ce ta samu a gidajen alƙalan, ta kuma gano wasu takardu na bayanai kan mallakar manyan rukunan gidaje.

Sai dai ya zuwa yanzu, hukumar ba ta iya gurfanar da dukkan alƙalan da wancan sumame ya shafa a gaban kotu ba.

Asalin hoton, NIGERIAN GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Majalisar kula da alƙalai ta ce gazawar babban lauyan gwamnatin ƙasar na kammala bincike da gurfanar da alƙali biyar a cikin shida ake zargi ta sanya ta ɗaukar wannan shawara.

Don haka Barista Sanusi ya ce "ba yadda za a yi a ci gaba da zama da su a dakace tun da babu wani zargi da ke kansu a gaban kotu."

A cewarsa idan ma akwai hanzari, to bai wuce na alƙali guda da wata kotu ta wanke shi ba, don kuwa har yanzu yana fuskantar wata shari'ah a kotun ɗa'ar ma'aikata.

Ya ce shi dai ba ya ganin wannan mataki a matsayin wani ƙoƙari na wanke alƙalan da ake zargi.

Lauyan ya ce "a wani ra'ayin... da zai fi kyau cewa su bar aiki gaba ɗaya tun da wataƙila jama'ar gari za su ga, an zarge su da wani abu kuma (ga shi) su koma, su ci gaba da yanke wa mutane hukunci."

"Kuma ko gobe ɓangaren zartarwa ya kammala bincike tare da gurfanar da su gaban kotu "dole za a sake dakatar da su".

A cewarsa, ba hurumin ɓangaren shari'ah ba ne ya je ya tambayi dalilan da suka sa har yanzu ba a gurfanar da mutanen da ake zargi a kotu ba.

Barista Sanusi Musa ya ce ɓangaren shari'ah ba ya aiki da abubuwan da aka rubuta a shafukan jaridu, sai an kai mutum gaban alƙali kuma an tabbatar da shaida kan zargin da ake yi masa.