Saudiyya ta rufe iyakarta da Qatar

Qatar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumomin Qatar ba su ce uffan ba kan batun ya zuwa yanzu

Saudiyya ta rufe iyakokin na ƙasa da sama da kuma ruwa da ƙasar Qatar, bayan ta zargi ƙasar da mara wa ta'addanci baya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito.

Qatar ta bayyana matakin da "rashin adalci" wanda "ba shi da tushe."

Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain sun bai wa duka 'yan kasar Qatar da suke zaune a ƙasashensu wa'adin mako biyu da su fice daga ƙasashensu.

Hakazalika, ƙasashen uku sun haramta wa 'yan ƙasarsu zuwa ƙasar Qatar.

Sai dai Saudiyya ta ce ba za ta hana alhazan Qatar halartar aikin hajjin bana ba.

Kawo yanzu dai babu alamun Qatar za ta mayar da martani.

Hulɗar Diplomasiyya

Saudiyya da Bahrain da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa da Masar sun katse hulɗar diplomasiyya da Qatar.

Sanarwa ta biyo bayan ƙaruwar tunzurin da ke akwai a yankin, tun bayan zargin kutsen da aka yi wa kamfanin dillancin labaran ƙasar Qatar a cikin watan jiya.

Bahrain dai yi ƙorafin cewa Qatar na yi mata katsalandan a harkokin cikin gida.

Yayin da ita ma, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zargi Qatar da yunƙurin wargaza tsaro a yankin Gulf.

Wannan dambarwa na zuwa ne, kimanin mako biyu bayan wasu kalamai masu cike da taƙaddama da ake alaƙantawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani da suka bayyana a shafukan intanet.

Gwamnatin ƙasar Qatar dai ta yi watsi da kalaman tana cewa na bogi ne.

Kasar Qatar

Babban birni: Doha

  • Jama'a Miliyan 2.7

  • Girma 11,437 murabba'in mita

  • Babban Harshe Larabci

  • Addini Musulunci

  • Hasashen rayuwa Shekara 97 (maza), 78 (mata)

  • Takardar kudi Riyal

Getty Images

Yaya tasirin wannan matakin zai kasance?

Kasar ta Qatar wacce take shirin daukar nauyin gasar kwallon kafa ta duniya a shekara ta 2022, ta soki wannan matakin da kasashen suka dauka.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce, "An dauki wadannan matakan ne a kan zargi maras tushe", kuma ta kara da cewa "wannan matakin ba zai shafi rayukan mutane da mazauna kasar ba".

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson yayi kira ga kasashen da su sasanta ta hanyar tattaunawa, a lokacin da yake mayar da martani a birnin Sydney na kasar Austireliya.

Asalin hoton, ALLSPORT/GETTY IMAGES

Kasuwar hannun jarin kasar ta Qatar ta fadi a safiyar Litinin saboda wannan matsalar.

Daya daga cikin abubuwan da zai iya tasiri shi ne batun samar da abinci: kashi 40 cikin dari na abincin da ke shiga Qatar daga Saudi Arabia ake shigar da shi.

Jaridar Doha ta rawaito cewa mutane sun yi ta ribibin sayen kayan abinci da ruwa a manyan shagunan kasar.