'Na shafe kwana 11 kafin na san mutuwar 'yata' bayan harin London

Emergency workers take a body on a stretcher from Russell Square tube station Hakkin mallakar hoto Getty Images

A lokacin da Sarah Jenkins ta ga hotunan iyayen da suke cikin tashin hankali suna neman bayanan 'ya'yansu wadanda suka bata bayan harin bam din da aka kai Manchester, sai ta tuno da halin da ta shiga shekara 12 da suka shude.

Ta zauna cikin halin bakin ciki na tsawon kwana 11 bayan da aka kai wani hari a ranar bakwai ga watan Yulin shekarar 2005 a Landan, kafin ta tabbatar da mutuwar 'yarta Emily. Saboda haka ne take rajin ganin an sanar da mutanen da 'ya'yansu suka bata cikakken bayani.

Sarah ta ce, "Emily ita ce 'yata ta hudu, kuma ita ce karama a cikin 'ya'yana. Wani lokacin tana da kiriniya, sai dai tana da raha".

A safiyar ranar bakwai ga watan Yulin shekarar 2005 ne abin ya faru, a lokacin Emily tana da shekara 24, tana kan hanyarta ta zuwa aiki a Landan.

Sarah tace, "Tana zaune tare da sabon saurayinta a arewacin Landan, har zuwa lokacin da babbar 'yata ta kira ni take ce mini, dukkanmu muna cikin koshin lafiya, sai dai Emily ce har yanzu ba ta dawo daga wurin aiki ba, amma wannan ba wani sabon abu ba ne, tunda ta sha kaiwa irin wannan lokacin ba ta dawo daga aiki ba".

Emily ba ta dawo ba har zuwa lokacin cin abincin rana, inda daga nan ne aka fara tsammanin ko dai ba lafiya ba.

Sarah ta shafe wannan safiyar a Clapham da ke kudancin Landan, inda daga baya ta tafi ofishin 'yansanda cikin halin rashin lafiya, a nan ne ta tarar da daya daga cikin 'ya'yanta. Biyu daga cikinsu kuma sun shiga wurin da ake kallon bidiyon tashin bam din kai tsaye a wata babbar akwatin talabijin.

"Abu na farko da suka fara yi shi ne kiran layin neman taimako," in ji ta.

"Bayanai kadan kawai aka samu saboda ba wani cikakken bayani."

Duk lokacin da suka kira wanda zai yi magana dabam, amma kuma tamboyi iri daya suke yi.

Da yamma ne suka hadu ita da sauran 'ya'yanta uku, amma ba su san takamaiman mai za su yi ba. Daga baya ne suka kira jami'in dan sanda, wanda ya shaida musu cewa su kira layin taimakon gaggawa, wanda dama suna ta kira ba adadi.

"Haka muka shafe wannnan daren muna ta kira, ba wanda ya yi bacci a cikinmu, muka ci gaba da kiran layin taimako kowa sai ya ce, kun tuntubi kawayenta?". In ji ta.

Sarah ta ce,"Kamar zan yi kururuwa."

Ana cikin wannan hali ne, sai danta James ya tashi tsaye ya ce ina ganin mu tafi asibitoci mu duba ko za a dace, amma sai ma'aikatan asibitin suka nuna musu wani daki suka ce su jira a nan.

Su dai sun san cewa Emily jirgin karkashin kasa take shiga idan za taje kudancin Landan , saboda haka sai suka garzaya zuwa tashoshin jirgin na King's Cross da Russell Square da niyyar samun bayanai. Amma duk da haka ba a samu nasara ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daya daga cikin abubuwan da Sarah tafi tunawa a wannan lokacin shi ne, yadda zuri'arsu suka tsauna cikin taraddadi, yadda danta Barnaby yake sayo biredi da yamma, amma ba wanda zai iya ci. Kullum sai sun fito da tarin biredin da suka kasa ci.

Duk tsawon wannan lokacin, Sarah tana sa ran Emily tana raye.

Bayan kwana uku ne, daga karshe iyalan Sarah suka tuntubi jami'in sadarwa. A nan dai an samu ci gaba, sai dai har yanzu Sarah ba ta san dalilin da yasa ba a gano 'yarta ba. A ranar Emely tana rike da katin cirar kudinta da kuma katin yin tafiye-tafiye. Ta saka wata sarka, an yi mata zanen da ake yi a jiki a bayanta, wadannan ne abubuwan da Sarah ta bayyana cikin nutsuwa.

Ta ce,"Suma sauran wadanda abun ya rutsa da su ba a gano su da wuri , amma dai ba kamar mu ba, don Emily ce ta karshen wacce aka gano".

Daga baya ne Sarah ta gane cewa 'yarta na cikin wadanda abun ya rutsa da su na farko da aka fito da su daga jirgin karkashin kasar.

Sarah tace, "Kafafunta ne kawai suka lalace a harin bam din, ban da wannan ba abin da ya sameta."

Image caption Sarah sanye da sarkar da Emily ta saka a ranar da ta mutu

A ranar da harin bam din ya cika kwana 11 ne , daga karshe jami'in dan sandan ciki ya zo ya sanar musu da mummunan labarin mutuwar Emily.

Daga baya ne, Sarah ta shiga aikin bayar da bayani ga 'yan'uwan da abun ya shafa bayan faruwar wani gagarumin hadari, kuma take aiki da ma'aikatar gwamnati a shirin da ake yi na kirkiro shafen da za a rika sanar wa da 'yan uwa asibitocin da ake kula da wadan da abun ya rutsa da su, da kuma samar da taikamo wajen shirya bikin binne su da, da kuma ba wa iyalansu diyya.

Ta ce, an yi mata alkawarin cewa za a kaddamar da shafin, sai dai bayan da aka kai harin bam din Mancherster ta fahimci cewa ba abin da ya sauya.

Tace tana jin takaicin yadda har yanzu 'yan uwa suke bin manyan tituna wajen neman 'yan uwansu, kamar yadda ta yi shekara 12 da suka gabata.

Za ta so wata hukuma su kirkiro shafin , domin samarwa da 'yan uwa bayanan idan wani al'amari irin haka ya faru. "Amma idan ba zasu iya haka ba, ko kuma ba wanda yake ganin shawara ce mai kyau, to ni zan yi, " in ji ta.

Ta ce za ta yi iya kokarinta don ganin shafin ya tabbata, ba za ta bari hakan ya tafi a iska ba. "Ina sa ran ganin wasikar amsa daga ofishin," a cewarta.

Labarai masu alaka