Mai ɗaukar hoton dake wa Afirka kwaskwarima

Duk lokacin da aka zo maganar hotunan afirka, hotunan da ake wallafawa sukan nuna wa mutanen dake wajen nahiyar cewa Afirka na fama da talauci da kuma tashe-tashen hankula.

To sai dai wani shafin Instagram na Afirka na kokarin sauya hakan. Baya ga rashin kula da wadancan hotuna, shafin kan yi kokarin nuna kyawawan abubuwan da ke nahiyar, da dawo da martabarta da kuma taimaka wa wajen sauya tunanin mutane game da nahiyar.

A nan mun bayyana wasu hotuna na baya-bayan nan da shafin ya tattaro na shafukan mutane daban-daban.

Hakkin mallakar hoto Tom Saater

Wani mai daukar hoto dan Najeriya mai suna Tom Saater, ya dauki hoton wata lauya mai suna Ginika Okafor wacce ba ta dade da ta zama barista ba.

Tana kan hanyarta ta zuwa bikin kammala karatu a babban birnin kasar Abuja, lokacin da aka dauke ta hoton tana cikin zurfin tunani.

Saater ya ce wannan babbar rana ce ga Ginika. Ta yi ta kuka lokaci kadan kafin a dauke ta hoton, kuma ta yi magana sosai game da yadda rayuwarta za ta kasance bayan kammala karatu, in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Ricci Shryock

Ricci Shyrock ta dauki hoton wannan mutumin, wanda ake goge wa takalma, duk kuwa da irinm kurar da titin ke da shi a babban birnin kasar Guinea wato Conakry, kafin kasar ta bayyana nasarar yakar cutar Ebola.

"Akwai wani abu da na fahimta game da wannan aikin da kuma goge takalma na tafiya daidai duk da ana jin tsaron Ebola", in ji ta.

Hakkin mallakar hoto Malin Fezehai

Malin Fezehai ya dauki hoton wadannan yaran lokacin da suke wasa a kusa da Zariya, da ke arewacin Najeriya.

"Ina son yaron da ke tsakiya, wanda ke kallo tare da lura da abubuwan da suke faruwa a kusa da shi", in ji ta.

"Har ila yau, akwai gajimaren da ya kawata hoton, saboda ga hadari nan ya hadu, kuma ina ganin kyakkyawan yanayin wajen wasa ne da nake matukar sha'awa".

Hakkin mallakar hoto Austin Merrill

Austin Merrill ya dauki hoton wasu yaran suna wasa, a wata makaranta a Mombasa da ke kasar Kenya.

" Ina jin cewa wannan hoton na da wani abu da za a iya fada game da makomar yaran a nan gaba," inji shi

Hakkin mallakar hoto Edward Echwalu

Edward Echwalu ya dauki hoton wani mai sana'ar dambe yayin da yake atisaye a wani dakin motsa jiki a Katanga da ke Kampala babban birnin Uganda.

Dakin motsa jikin wuri ne da mata ke zuwa domin dambe. Da farko dai suna yi ne domin kare kansu, amma wasu matan kan yi amfani da shi wajen samun kudi.

"Ana yi wa dambe kallon wasa ne da ya shafi maza kadai, amma wadannan mata sun sauya wancan tunanin," in ji Echwalu. "A ganina matashin da ke hoton ya fahimci cewa dambe ba na maza ba ne kadai."

Hakkin mallakar hoto Laura el-Tantawy

Rigar karfe tare da gashi da wannan karamar yarinya 'yar gudun hijira a garin Mugungu, da ke gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, ta dauki hankalin Ley Uwera, wata mai daukar hoto.

Ta ce "Yadda ta gyara gashinta, da yadda ta ke kallo cikin nitsuwa ne suka dauki hankalina"

"Hoton ya nuna cewa kowa zai iya rayuwarsa cikin sauki. Ya nuna akwai alamun jin dadi game da yanayin, wanda ba shi da wani aibu sosai".

Hakkin mallakar hoto Jana Asenbrennerova

"Kasancewa cikin zulumi yayin rubuta jarrabawa, wani abu ne da ya zama ruwan dare tsakani dalibai," in ji wata mai daukar hoto mai suna Jana Asenbrennerova.

Ta dauki hoton wadannan daliban ne a Jami'ar Kinshasa da ke babban birnin Jamhuriyar dimokradiyyar Congo, yayin da suke rubuta jarrabawarsu ta karshe.

Hakkin mallakar hoto Andrew Esiebo

Wayar salula kan taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da shafin Instagram na Afirka. Wannan hoto ne da Andrew Esiebo ya dauka,

Wadanna kyawawan 'yan matan biyu ne a wani kanti da ke Legas suna daukar hotunan kansu yayin da suke shirin fita da daddare.

Hakkin mallakar hoto Charlie Shoemaker

Charlie Shoemaker ya ce, "Na dauki wannan hoto ne a a lokacin bazara da rana a mako na karshe a lokacin bikin al'ada a birnin Cape Town,"

"Titunan kasar sun cika makil da masu busa kakaki tare da masu rawa, haka shi ma titin da ke birnin ya cika makil."

Shoemaker ya ce: "Hoton na nuna mutanen na cikin yanayin annashuwa".

Hakkin mallakar hoto Holly Pickett

Holly Pickett wani mai daukar hoto ne, ya ce yana wani aiki ne a Sare Dembara da ke kudancin Senegal, lokacin da ya kuduri aniyyar daukar hotunan wasu mazauna kauyen.

"Matashin da ke hotan ya yi sauri ya dauki 'yarsa kafin ya zo gare ni domin daukar hoton."

"Kuma yana cike da alfahari, yana so a dauke shi tare da ita, yan matukar sonta, tare da kaunarta. kai son iyaye game da yara yana nan ko'ina".

Hakkin mallakar hoto Nichole Sobecki

An kawo Nichole Sobecki zuwa wannan dakin daukar hoton a Kibera, wani babban gari a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, yayin da haske ke haskakawa da sanyin safiya.

Ana yi wa wannan yaron hoton katin ID card.

"Dalibai kan dauki hoton ne saboda bukata kamar yadda da yawa daga cikinmu muke daukarsa saboda wani amfani," inji ta.

Hakkin mallakar hoto Jane Hahn

In Mali's capital, Bamako, in November 2015, while attention was focused on the aftermath of an Islamist militant attack on a hotel, life carried on as normal elsewhere in the city.

A Bamako, babban birnin kasar Mali a watan Nuwambar 2015, yayin da hankali ya karkata kan illolin da hare-haren da kungiyar masu tada kayar baya suka kaddamar a wani otel, rayuwa ta fara inganta ko'ina a birnin.

Ga Jane Hahn, hoton da ta dauka na wannan matar da ke tuka babur, yayin da iska ke kada gashin kanta, "hoton na nuna juriya, da karfi, da kuma kyau da mutanen Mali ke da shi".

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba