'Burina auren mata huɗu ya ci gaba da karɓuwa'

Musa Mseleku and his four wives on a South African reality TV show Hakkin mallakar hoto Mzansi Magic
Image caption Musa Mseleku tare da matansa hudu

Wani sabon shirin talabijin wanda yake nuna muhimmancin auren mata huɗu ya jawo muhawa kan al'adar auren fiye da mace ɗaya a ƙasar Afirka ta Kudu.

Mai gabatar da sabon shirin, Musa Mseleku, wanda a zahiri yake da mata hudu, ya ce an kirkiro shirin ne don a sauya tunanin mutane game da auren mace fiye da daya. Ya ce yana samun taimako yayin gabatar da shirin daga duka matarsa hudu.

Magidanci mai shekara 43 injiniyan gine-gine ne. Yana gabatar da shirin talabijin din ne tare da matansa hudu da kuma 'ya'yansa 10. Sunan shirin Uthando Nes'thembu wanda yake nufin "Soyayya da kuma Auren Mace Fiye da Daya"

Shirin wanda aka fara a ranar 19 ga watan Mayu, ya kasance wani abu da ake yawan maganarsa a shafin sada zumunta na Twitter a kasar Afirka ta Kudu. Inda wasu suke muhawara kan matsayin al'adar auren fiye da mace daya a wannan zamanin.

Ana daukar wasan ne a kauyen Mseleku kusa da birnin Durban. Kowace daga cikin mata hudun tana da gidanta daban ne a wasan.

Mista Mseleku ya ce: "Daya daga cikin mummunar fahimatar da wasu suke yi wa auren fiye da mace daya shi ne yadda suke ganin al'ada ce da ke danne hakkin mata."

Ya ce wannan dalilin ne ya sa "muka kirkiri shirin saboda mutane su fahimci cewa a wurinmu abin ba haka ba ne," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "ina so na nuna wa maza cewa za ka iya auren mace fiye guda kuma ka kasance mai gida."

Sai dai ba kowa ba ne ya amince da hakan. Yayin da wasu suke nuna jin dadinsu ga shirin, wasu kuma suna sukar shirin ne.

Wasu ma'abota shafin Twitter galibinsu mata suna sukar shirin musamman wata rana da Mseleku ya sanya wa matansa dokar hana fita daga karfe biyar na yamma. Hazalika, sai sun nemi izininsa idan za su je wurin abokansu ko kuma idan za su sha barasa.

Hakkin mallakar hoto Mgazi Magic
Image caption Musa da iyalansa

Amaryar Mseleku ta karshe, Thobile Mseleku, ta ce: "Na yi amannar cewa a kowane gida musamman a Afirka ta Kudu, mun dauki miji tamkar ubangiji. Saboda haka ba zai yiwu mu yi abin da muka so ba, ba tare da ya sanya mana albarka ba."

Musa Mseleku ya ce shi kansa akwai dokokin da ya sanya wa kansa. Ya ce saboda haka ne yake taya su wasu aikace-aikacen gida.

Musa ya auri Thobile ne kimanin shekara tara da suka wuce. Yana da mata biyu lokacin da suka fara haduwa da ita, don haka Thobile tana sane da irin gidan da za ta shiga.

Hakazalika, Thobile ta ce kakanninta su ma sun kasance suna da mace fiye da guda.

Har ila yau, ta ce ita ta dauki sauran matan - wato Busisiwe MaCele da Nokukhanya MaYeni da kuma Mbali MaNgwabe tamkar 'yan uwanta na jini ne kuma tana samun shawarwari da taimako daga gare su.

Hakkin mallakar hoto Mzansi Magic
Image caption Matan Musa ke nan. Thobile ta ce da wuya ake jin kansu kuma su tamkar 'yan uwan juna ne

Shirin yan nuna yadda matan hudu suke tafiyar da harkokin gidan Musa, wasu daga cikinsu ma'aikatan gwamnati ne, wasu kuma 'yan kasuwa ne. Aikace-aikacen gida da kuma tarbiyar yara su ne abubuwan da suke kawo kace-na-ce a gidan.

"Babban damuwarmu bai wuce maganar lokaci ba," in ji Thobile Mseleku. "Akwai matsala idan muka ce dukanmu za mu fita tare saboda idan mutum daya ya shirya zai yi aiki sai ya jira saura."

Musa ya ce lokaci ne abin da yake ransa a kodayaushe.

"Ina iya kokarina don tabbatar da cewa na raba lokaci ga duka matana da 'ya'yana daidai wa daida."

Hakkin mallakar hoto Mzansi Magic
Image caption Musa Mseleku ya ce 'ya'yansu suna cikin farin ciki da annashuwa

A Afirka ta Kudu, galibin mutane ba su cika auren fiye da mace daya ba - yin hakan ba wai ya saba wa doka ne ba, kuma ba mabiya wani ne kawai suka keɓanta da yi ba.

Kodayake 'yan kabilar Zulu sun fi raya al'adar auren mace fiye da daya, kuma Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma kansa dan kabilar Zulu ne, hakazalika yana da mata uku ne.

Wani malami a Jami'ar KwaZulu-Natal, Ndela Ntshangase, ya ce auren fiye da mace daya a Afirka ta Kudu ya fara raguwa a karni na 19 lokacin da Turawan mishan suka bukaci masu koma wa addinin Kirista su zabi mace daya cikin matansu wadda za su ci gaba da zama da ita, kafin su ba su addinin Kirista.

Ya ce: "Turawan mulkin mallakar Birtaniya sun tilasta wa bakake kasancewa masu mata daya ta hanyar sanya haraji ga kowace mace da mutum ya kara. Da kuma bayar da kankanin filin gina gidaje wanda ba zai isa masu mata da yawa."

Amma me zai faru idan aka juya labarin Musa Mseleku? Wato ko zai yarda idan daya daga cikin matansa ta kara auren wani mijin?

Sai ya ce: "A'a,'' cikin dariya, ''Zan mutu ke nan!"

Thobile ta ce dabi'un mijinta ba sa damunta.

"Mu muka zabi wannan rayuwa. Mun zabe shi kuma shi kadai," in ji ta.

Daga nan, an tambayi Musa shin ko zai iya kara mace ta biyar?

Sai ya ce: "Muna duba wannan batun a shirin don haka ku ci gaba da kallon shirin."

Labarai masu alaka