Tsohon ministan lafiyar Nigeria Babatunde Osotimehin ya rasu

Babban Darakta a hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA), Farfesa Babatunde Osotimehin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babatunde Osotimehin ya rike mukamai da yawa a ciki da wajen Najeriya

Tsohon ministan lafiya na Najeriya, kuma Babban Darakta a hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA), Farfesa Babatunde Osotimehin ya rasu.

Wata sanarwa da UNFPA ta fitar a madadin iyalin marigayin, ta ce ya rasu ne a ranar Lahadi, yana da shekara 68.

Marigayin ya mutu ne a birnin New York na Amurka, inda ofishinsa ya ke.

Sanarwar ba ta bayyana sababin mutuwar tasa ba, amma dai ta ce iyalansa sun "nuna godiya ga Allah kan tsawon rai" da kuma nasarorin da ya bashi a rayuwarsa ta duniya.

Ya rike mukamin ministan lafiya a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010.

Sai a nan gaba ne za a bayyana lokaci da kuma inda za a binne marigayin.

Mista Osotimehin ya rike mukamai da yawa a ciki da wajen Najeriya, kuma yayi karatu a wasu kasashen waje ciki har da Ingila.