Nigeria: Shugaba Buhari ya kusa dawowa, in ji matarsa Aisha

Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari
Image caption Aisha Buhari ta shafe mako guda a London inda mijinta ke jinya

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce mijinta na murmurewa sosai kuma nan gaba kadan zai komo gida daga jinyar da yake yi a kasar Ingila.

Tana magana ne a safiyar Talata bayan da ta dawo daga London, inda ta kai masa ziyarar mako guda.

Wata guda kenan da shugaba Muhammadu Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar zuwa Birtaniya - wacce ita ce tafiyarsa jinya karo na biyu a bana.

Hajiya Aisha ta ce shugaban ya "godewa 'yan kasar kan addu'o'in da suke yi masa da kuma goyon bayan da suke bai wa Mukaddashinsa Yemi Osinbajo".

Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

Rashin lafiyar Buhari

Me kuka sani?

Yuni 2016

Ya tafi London don jinyar ciwon kunne inda ya shafe mako biyu.

Janairu 2017

Ya sake tafiya London inda ya shafe mako bakwai yana jinya.

 • Maris 2017 Ya koma Najeriya inda yace bai taba rashin lafiya kamar wannan ba.

 • Mayu 2017 Ya sake tafiya London kuma har yanzu yana can.

 • Yuni 2017 Matarsa Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai bayan da ta ziyarce shi.

Getty

Rashin lafiya ta mamaye rayuwar Buhari a 2017

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin lafiyar da yayi a farkon bana ta tsananta sosai
 • 19 ga watan Janairu ya tafi Birtania hutun jinya
 • 5 ga watan Fabreru ya nemi majilisa da ta tsawaita hutun nasa
 • 10 ga watan Maris ya dawo gida to sai dai bai koma aiki ba kai tsaya
 • 26 ga watan Afrilu ya kasa halartar taron majalasar zartarwa karo na biyu, inda ya rinka "aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afurilu bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu bai halarci taron majalisar zartarwa ba karo na uku jere
 • 5 ga watan Mayu ya halarci Sallar Juma'a a Abuja
 • 6 ga watan Mayu ya sake tafiya Birtaniya neman magani
 • 6 ga watan Yuni Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai

Labarai masu alaka