An kama 'yan China 31 a Zambia

Ma'adanai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kanfanonin kasar China sun zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a fannin hakar ma'adanan a Zambia.

An kama wadansu 'yan China 31 a Zambia bisa zarginsu da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Sai dai China ta yi Allah-wadai da matakin kuma ta ce Zambia ba ta bayar da wasu kwararan hujjoji ba game da kamen.

Ministan harkokin wajen Chinar ya ce "Daga cikin wadanda ake rike da su har da mata masu juna-biyu da kuma wasu mutane biyu da suka kamu da zazzabin cizon sauro''.

Hakazalika, Darakta Mai kula da harkokin Afirka a ma'aikatar harkokin wajen kasar China Lin Songtian ya nuna damuwar shi game da makomar dangantakar diplomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.

China na nuna goyon baya game da kawar da hakar ma'adainai ba bisa kan ka'ida ba.

Har ila yau, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Chinar Hua Chunying ya ce: "China ba ta goyon bayan nuna bambanci kan 'yan wasu kasashe wajen aiwatar da dokar ta yadda ake kama 'yan kasar ta ba tare da wasu hujuji masu karfi ba''.

Kanfanonin kasar China sun zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a fannin hakar ma'adanan a Zambia.

A shekara ta 2012 masu hakar ma'adanai a Zambia sun kashe wani jami'in kasar China yayin wani rikici game da biyan albashi a wata mahakar gawayi.