Kun san tarihin marigayi Babatunde Osotimehin?

Babatunde Osotimehin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babatunde Osotimehin ya kawo sauye-sauye a hukumar da ke yaki da cutar kanjamau ta Najeriya

Farfesa Babatunde Osotimehin, wanda ya rasu ranar Lahadi, ya rike manyan mukamai, cikinsu har da ministan lafiya na Najeriya.

Marigayin, wanda a lokacin rasuwarsa, shi ne shugaban hukumar kula da yawan al'umma ta majalisar dinkin duniya (UNFPA), ya mutu ne a birnin New York na Amurka yana da shekara 68.

An haifi Farfesa Osotimehin a shekarar 1949 a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Ibadan, sannan ya yi digirin digirgir a Jami'ar Birmingham da ke Ingila a 1979.

Cikin manyan mukaman da ya rike har da shugaban Kwalejin koyar da aikin likita da ke Jami'ar Ibadan tsakanin 1990-1994.

Kafin nan kuma ya koyar a Jami'ar ta Ibadan a shekarun 1980.

Farfesa Osotimehin ya zama Darakta Janar na hukumar da ke yaki da cutar kanjamau ta Najeriya, NACA daga watan Maris na 2007 zuwa watan Disamba na 2008.

Kazalika ya zama shugaban kwamatin kasa da ke yaki da cutar kanjamau a Najeriya tsakanin 2002 -2007.

Ya rike mukamin ministan lafiya a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'adua daga shekara ta 2008 zuwa 2010.

Marigayin ya rubuta littattafai da makaloli da dama a kan harkokin likitanci da kiwon lafiya.

Farfesa Osotimehin, mamba ne a kungiyoyi daban-daban da suka shafi harkokin lafiya, cikinsu har da Royal College of Physicians (UK), Harvard Centre for Population and Development Studies, Cambridge da kuma International Advisory Group, Population and Reproductive Health.