Dogara zai yi dambe da Mayweather

Floyd Mayweather Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Floyd Mayweather ya yi nasara a kan 'yan dambe da dama ciki har da Manny Pacquiao

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara zai fafata da fitaccen dan damben nan na Amurka da ya yi ritaya Floyd Mayweather.

Mutanen biyu za su yi damben ne ranar Laraba, 14 ga watan Yuni a otal din Transcorp Hilton, Abuja.

Za su barje gumi ne a wani yunkuri na tattara gidauniyar kudi.

Shugaban rukunin kamfanonin Tetrazzini, Donatus Okonkwo, wanda ya bayyana hakan a wurin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, suna fatan karawar za ta yi armashi.

Tetrazzini shi ne ke gudanar da Zinni media, wadanda suka shirya ziyarar kwana uku ta bikin damben boksin a Najeriya.

Ana sa ran Mayweather zai kai ziyara Lagos, Anambra, Akwa Ibom da Abuja inda zai gana da bangaren zartarwa da majalisar dokoki.

Rahotanni sun ce Yakubu Dogara ya amince ya fafata da tsohon dan damben.

Labarai masu alaka