Wacce riba Nigeria za ta samu da shigar Morocco ECOWAS?

Sarki Mohammed na Moroko Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Morokon ta fice daga kungiyar tarrayar Afirka ne a 1984 bayan da aka tabbatar da yankin Yamacin Sahara

Wasu masu sharhi kan harkokin diplomasiyya sun yi zargin cewa ƙoƙarin ƙasar Morocco na shiga ƙungiyar raya tattalin arziƙin Afirka ta yamma ECOWAS, wata maƙarƙashiya ce ga Nijeriya.

Tsohon Jakadan Nijeriya a ƙasar Sudan Ambasada Suleiman Dahiru ya ce "akwai 'yan guna-guni cewa Nijeriya ta ƙarfi da yawa, ina gani makircin da aka yi shi ne a kawo Morocco don a rage ƙarfin Nijeriya."

Ana kallon Nijeriya a matsayin giwar Afirka ta fuskar yawan al'umma da tattalin arziƙi.

Ya kuma ce: "Akwai ƙasa 15 a ƙungiyar ECOWAS, amma babu ƙasa ɗaya a cikinsu da ta hada iyaka da Moroko."

A cewarsa shigar "bare" zai farraƙa kan mambobin ƙungiyar, don kuwa ba kowa ne zai yarda da ita ba.

Sai dai, a baya-bayan an ga Morocco da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa hulɗar da ke tsakaninsu, ta hanyar kasuwanci da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ko a watan Disamban shekara ta 2016, Sarki Mohammed na Morocco ya kai ziyara Nijeriya, inda ya sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi da gwamnatin ƙasar.

ECOWAS dai ta yi maraba Morocco a matsayin mamba cikin ƙungiyar duk da yake Morocco na can ɓangaren ƙasashen arewacin Afirka ne.

Su dai shugabannin ECOWAS yayin wani taro a Liberia cikin shekara ta 2017, sun ce dole sai duk 'ya'yan ƙungiyar sun amince kafin Morocco ta zama cikakkiyar mamba.

Ambasada Suleiman Dahiru ya ce Morocco na son shiga ECOWAS ne don biyan buƙatar bunƙasa tattalin arzikinta, amma ba don taimaka wa ƙasashen kungiyar ba.

"Abin yana da ɗaure kai idan aka dubi ƙasashen da suka ƙirƙiro ƙungiyar, baya ga biyar da ke yaren Ingilishi duk sauran yaren Faransa ne. Ina ga akwai makirci na neman rage wa Nijeriya karfi a cikin kungiyar."

Ambasada Dahiru ya kuma kara da cewa idan ba an maida hankali ba kungiyar ECOWAS ko bata ruguje to za a samu mummunan rudani da zai mayar da hannun agogo baya a cikin al'amuran kungiyar.

A farkon shekarar 2017 ma, Morocco ta sake komawa ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) bayan ta fice a shekarar 1984.

An tambayi masanin harkokin diplomasiyyar ko da wanne za a kira ƙungiyar ECOWAS, bayan Morocco ta zama cikakkiyar mamba, sai ya ce sunan ƙungiyar ba shakka ya sauya.

"Amma, ni ban san yadda za a kira ta ba kuma."

Labarai masu alaka