'Yan sanda sun bayyana biyu daga cikin maharan London

London Suspected attackers Hakkin mallakar hoto MET POLICE
Image caption 'Yan sanda da hukumar tsaro ta MI5 sun kwan da sanin Khuram Butt (hagu)

'Yan sanda sun bayyana sunayen mutum biyu a cikin uku da suka kai harin daren Asabar a birnin London.

'Yan sanda da hukumar leƙen asiri ta MI5 sun kwan da sanin matashi ɗan shekara 27, haifaffen Pakistan, Khuram Butt, na yankin Barking a London, sai dai babu wani bayanin sirri da suke da shi da ke alaƙanta shi da wani hari.

Sai ɗaya maharin, Rachid Redouane, mai shekara 30 daga yankin Barking, wanda 'yan sandan suka ce ya yi iƙirarin shi ɗan asalin Morocco da Libya ne.

'Yan sanda sun dai harbe waɗannan mahara. Kuma a yanzu an saki duk mutum 12 da da aka kama bayan kai harin ba tare da an tuhume su ba.

An kama mata bakwai da maza biyar a unguwar Barking ranar Lahadi bayan kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai wasu 48 suka ji raunuka.

Maharan sun tuƙa motar ɗaukar kaya ta haya cikin matafiya na gefen hanya a kan Gadar London kafin kuma su riƙa caccaka wa mutanen da ke yankin Kasuwar Borough wuƙa.

An gudanar da taron nuna alhini a dandalin Potters Field kusa da Gadar London a maryacen ranar Litinin don mutanen da wannan hari ya ritsa da su.

Hukumar kula da lafiya ta Burtaniya ta ce mutum 36 suka rage kwance a asibiti, 18 suna cikin mawuyacin hali.

Redouane, wanda ƙwararren kuku ne, yana kuma amfani da sunan Rachid Elkhdar. 'Yan sanda ba su san shi ba, kafin kai harin.

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Mark Rowley ya ce: "ana ci gaba da bincike don tabbatar da ko wane ne abokin aikata laifin nasu."

Ya kuma ce: "Ana ci gaba da aiki don ƙara fahimtar su wane ne mutanen, da alaƙar da suke da ita da kuma ko sun samu tallafi ko goyon bayan wani mutum daban."

An ga Butt a wani dogon rahoto na talbijin ɗin Channel 4 a bara game da masu tsaurin ra'ayin addini da dangantakarsu da wani mai wa'azi da aka ɗaure Anjem Choudary.

An ga Maharin, wanda ke da yayye da mata da kuma aƙalla ɗa ɗaya a cikin shirin yana musu da 'yan sanda a kan titi.

BBC ta gano Butt darakta ne a wani rusasshen kamfani da ake kira Kool Kosmetics.

Labarai masu alaka