Qatar na neman sulhu da kasashen Larabawa

Taswirar hanyar da jiragen Qatar Airways ke bi a ranar Talata, 6 ga watan Yuni

Asalin hoton, FlightRadar24.com

Bayanan hoto,

Na'ura mai bibiyar jirage a sararin samaniya ta FlightRadar24 ke nuna takaitacciyar hanyar da jiragen sama na Qatar Airways ke bi da safiyar Talata

Qatar na goyon bayan tattaunawa da makwabtanta ta hanyar diflomasiyya bayan rikicin da ya barke tsakaninsu.

Kasashe da dama sun yanke hulda da Qatar, suna tuhumarta da tallafa wa ta'adanci a yankin mashigar ruwa na Gulf.

Makwabtan kasashen da suka hada da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun dakatar da jiragen kasar Qatar ratsawa cikin sararin samaniyarsu.

Kasar Kuwait wacce ita ma tana cikin kasashen Larabawa amma rikicin bai shafeta ba, tayi tayin shiga tsakani, kuma Qatar ta yi na'am da tayin.

A cikin wata hira da tashar talabijin ta al-Jazeera, ministan harkokin wajen kasar ta Qatar ya sanar da cewa Sarkin Kuwait zai je Saudiya ranar Talata kan batun.

Sheikh Mohammed Bin Abdulrahman al-Thani ya shida wa al-Jazeera cewa Qatar na neman tattaunawar ta kasance anyi ta "a baiyane kuma kan gaskiya".

Bahrain da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Yamen da gwamnatin dake gabashin Libya da kuma Maldives sune kasashe 6 da suka katse huldar diflomasiyya da Qatar a ranar Litinin.

Kasashen Bahrain da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bai wa 'yan kasar Qatar mako biyu da su fice daga kasashensu, kuma sun hana 'yan kasashensu yin balaguro zuwa Qatar.

A ranar Talata Saudiya ta janye lasisin kamfanin jirgin sama na Qatar Airways, kuma ta umarci a rufe kamfanin cikin sa'o'i 48.

Mazauna kasar sun fara tara kayan masarufi domin tunkarar matsalolin karancin abinci da ka iya biyo bayan wannan matakin.

"Jama'a sun cika shaguna suna sayan kayan abinci, musammam irin wanda ake shigowa da shi daga waje", in ji wani mazaunin birnin Doha mai suna Eva Tobaji, a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters. "Lamarin ya yi muni, ban taba ganin irin wannan al'amarin ba''.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mazuna kasar suna tara ruwan sha ranar Litini