Nigeria: Kotu ta bai wa gwamnati miliyan $43 da aka gano a Legas

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon yadda EFCC ta gano kudin da ba ta taba gano irinsu ba

Wata babbar kotu a Najeriya ta halalta wa gwamnatin kasar fiye da dala miliyan 43 da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gano a wani gida da ke birnin Ikoyi, na Legas.

Mai shari'a Muslim Hassan ya ce a mika miliyoyin dalolin da hukumar EFCC ta gano a watan Afrilu ne sakamakon rashin samun wani da ya fito domin ikirarin mallakarsu.

Babbar kotun ta ce babu wani sashi da ya bayar da gamsassun hujjoji da za su nuna kudin, wadanda suka kai naira biliyan 13, mallakarsu ne.

Jim kadan bayan gano kudin, rahotanni sun ambato hukumar leken asirin kasar ta NIA tana cewa nata ne, abin da ya haifar da rudani a kasar.

Kudaden, wanda EFCC ta gano a rukunin gidajen Osborne, sun hada da dala miliyan 43, da fam 27,000 da kuma naira miliyan 23.

Jama'a da dama sun yi mamakin yadda za a boye zunzurutun miliyoyin daloli a lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki da rashin wadatattun kudaden kasar waje.

Ita dai hukumar ta NIA ta ce ta ajiye kudin ne domin wasu ayyuka na musamman da aka yi tanadinsu tun zamanin tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.

Hakan ne kuma yasa Shugaba Buhari ya dakatar da shugaban hukumar domin a gudanar da bincike a kan lamarin.

Itama dai gwamnatin jihar Rivers ta fito ta ce kudaden nata ne, to amma ba ta kafa hujjar yadda ta mallake su ba, sai dai kawai ta yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar ne ya boye su.

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta zargin da cewa siyasa ce kawai.

Dama dai babbar kotun ta bayar da zuwa ranar 5 ga watan Mayu ga duk wani da ke ikirarin cewa kudaden mallakarsa ne da ya zo ya kafa hujja, lamarin da ya gagara.

Najeriya dai na fama da matsalolin cin hanci, inda ake zargin wasu shugabanni na wawure dukiyar jama'a domin azurta kawunansu.