Iran: IS ta kai harin kunar-bakin-wake kabarin Khomeini

hoton na nuna hari a wajen fadar Hakkin mallakar hoto JamaranNews/Fars
Image caption Wannan hoton da Fars News ta wallafa, na nuna cewa harin ya auku ne a wajen hubbaren na Khomeini

'Yan bindiga sun afka wa kabari ko hubbaren Ayatollah Khomeini da majalisar dokokin kasar Iran, a babban birnin kasar Tehran, inda mutum bakwai suka rasa rayukansu.

An yi ta jin karar harbe-harbe daga na'urorin daukar sauti da ke wajen majalisar, haka kuma akwai rahotonnin da ke cewa an kashe mai gadin ginin.

Mutane da dama sun jikkata a ginin da ke Kudancin Tehran, wanda aka sadaukar ga jagoran jamhuriyar Musuluncin.

Daga cikin maharan akwai dan kunar bakin wake daya, tare da 'yan bindiga biyu, ko uku.

Gwamnan birnin Tehran ya ce daya maharin ya mutu ne sakamakon tashi bam din, yayin da dayan ya mutu sakamakon harbinsa da jama'an tsaro suka yi.

Ali Khalili, wani jami'in hulda da jama'a a fadar ta Khomeini, ya fada wa wata kafar yada labaran kasar cewa, daya daga cikin maharan ya tayar da bam din da ke jikinsa a gaban wani banki da ke wajen fadar.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Far ya rawaito cewa mace ce 'yar kunar bakin waken.

Hotunan ragowar jikin mahariyar sun nuna cewa tana sanye da bakaken tufafi ne.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin, amma ba ta bayar da wata hujja ba.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani yaro ana sakko da shi daga wani dogon gini
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana samun rahotanni masu karo da juna kan abin da ke faruwa a hubbaren

Labarai masu alaka

Labaran BBC