Mozambique ta dakatar da sayen kaji daga Zimbabwe

Gonar kiwon tsuntsaye a Zimbabwe Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasar Mozambique ta hana shiga da kaji kasar daga Zimbabwe mai makwaftaka da ita.

Haramcin ya biyo bayan bullar murar tsuntsaye ce a wata gona da ke Mashonaland a Gabashin kasar.

Ita dai wannan kwayar cutar da aka fi sani da H5N8, tana yawan afkawa tsuntsaye.

Lamarin dai ya sa an kashe tsuntsaye sama da 715,000 a Zimbabwen.

An gano nau'in cutar da dama, amma na Mashonaland ya fi tsauri da kuma illa.

Tun da farko a ranar Talata, itama kasar Botswana ta sanar da daukar irin wannan mataki.

Labarai masu alaka