Zan sauya dokar 'yancin bil'adama kan yaki da ta'addanci — May

Theresa May Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muddin dokar 'yancin biladama ta yi kokarin kawo ga yaki da ta'addanci, to lallai za mu sauya ta in ji Theresa May

Fira ministar Burtaniya Theresa May, ta ce a shirye take ta sauya dokokin kare 'yancin bil'adama da ke yin karan tsaye ga yunƙurin jami'an tsaro wajen ɗaukar ƙwararan matakai a kan barazanar ta'addanci.

Ƙusoshin jami'iyyarta ta Conservative sun yi nuni da cewa muddin aka sake zaɓen Mrs May a ranar Alhamis, gwamnatinsu a shirye take ta fice daga duk wasu tanade-tanaden Tarayyar Turai a kan 'yancin bil'adama.

A wani jawabin yaƙin neman zaɓenta na ƙarshe, Mrs May ta ce tana son ta sassauta ƙa'idojin hana wa wadanda ake zargi da aikata ta'addanci 'yancin walwala, tare da tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali.

Mrs May din ta ce za ta sauya dokokin yancin biladamar ne muddin suna kawo cikas ga kokarin shawo kan matsalar wadanda ake zargi da aikata ta'addanci.

Fira ministar ta ce za ta sassauta damar yi wa 'yancin mutanen da ake zargi da yunƙurin kai harin ta'addanci tarnaƙi, tare da iza ƙeyarsu zuwa ƙasashen da suka fito.

Batun tsaron dai ya kankane kwanakin karshe na yaƙin neman babban zaɓen da za a gudanar, bayan hare-haren ta'addancin da aka kai a biranen London da Manchester.

Yayin da take jawabi bayan harin London, Mrs May ta ce: "tura ta kai bango. Dole abubuwa su sauya" a yaƙin da ake yi da ta'addanci.

A wani jawabin kuma da ta gabatar ga masu fafutuka a garin Slough da ke Yammacin London a ranar Talata, Theresa May ta bayyana cewa yayin da ake ƙara ganin barazanar 'yan ta'addar na fitowa fili, akwai bukatar tabbatar da cewa jami'an tsaron ƙasar sun samu ƙarfin ikon da za su dauki matakai:

"Ina nufin zan yankewa waɗanda aka samu da laifin aikata ta'addacin dauri na tsawon lokaci a gidan yari. Ina nufin saukaka wa 'yan sanda damar samun iza ƙeyar baƙi wadanda ake zargi na yunƙurin aikata ta'addanci zuwa kasashensu.''

"Kuma ina nufin hana 'yancin walwala ga waɗanda ake zargi da ayyukan ta'addancin. A lokacin da muke da ƙwararan shaidun da suka nuna cewa su barazana ce ga kasa, amma kuma babu ƙwararaan shaidun da za mu iya gurfanar da su kacokam a gaban kuliya." Muddin dokar yancin bil'adama ta yi kokarin kawo mana cikas, to lallai za mu sauya ta."

A wata hira da jaridar The Sun, Mrs May ta kuma ce za kuma ta yi la'akari da tsawaita lokacin da za a rike mutanen da ake zargi, bayan rage kwanakin daga 28 zuwa kwanaki 14 a shekara ta 2011.

Labarai masu alaka