Shugaba Donald Trump zai sasanta Saudiyya da Qatar

Shugaban Amurka Donald Trump da Sarki Tamimi Bin Hamad na Qatar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Trump a ganawarsa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Than a cikin watan Mayu

Shugaba Donald Trump ya zanta da Sarki Salman na Saudiyya ana tsaka da fuskantar ƙaruwar rikici a kan Qatar, a wani yunkuri na sansanta rikicinta da Saudiyyar da sauran kasashen yankin Gulf.

Da farko shugaban ya yaba wa yunƙurin masarautar na mayar da maƙwabciyarta saniyar ware kan zargin samar da kuɗi ga masu tsaurin ra'ayin addini.

Sai dai fadar White House ta ce Amurka na tuntuɓar duk ɓangarorin, a ƙoƙarinta na shawo kan wannan dambarwa tsakanin manyan ƙawayenta, a lokaci guda kuma Pentagon ta yaba wa Qatar, saboda bayar da matsuguni ga sansanin sojin saman Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya.

Shi ma, shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ba da tayin shiga tsakani.

A wasu sakonni da ya rika wallafawa a shafinsa na Twitter a safiyar Talata, Mr Trump ya zargi kasar ta Qatar da bayar da tallafin kudi wa ayyukan ta'addanci.

A wata hira ta wayar tarho da Sarki Salman, Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Mr Trump na cewa, yana da matukar muhimmanci kasashen yankin Gulf su hada kawunansu don yaki da masu tsattsauran ra'ayi, da wanzuwar zaman lafiya a daukacin yankin.

Kasashe da dama ne dai a yankin tekun Gulf suka yanke huddar diplomasiyya da ta sufuri da Qatar din ranar Litinin.

Kasar Qatar din dai na musantawa da babbar murya zargin da ake yi mata na tallafa wa masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Image caption Ministan harkokin wajen Qatar: 'Babu wata shaidar cewa muna tallafawa 'yan ta'adda'

Sarkin Kuwait ne dai ke shiga tsakani a wananna takun saka, kana shugaban Turkiyya shima ya yi tayin bayar da taimako, da cewa yanke hudda da takunkumi ba za su kawo karshen tashin tashinar ba.

A baya-bayan nan ne dai Mr Trump ya yi ikirarin cewa kokarinsa ne ya haifar da daukar matakin da kasashen suka yi kan kasar ta Qatar, bayan wata ziyara da ya kai kasar Saudia Arabia a kwanakin baya.

Ministan harkokin wajen Saudi Adel Al-Jubeir ya yi kira ga kasar Qatar ta yanke hudda da kungiyar Hamas ta Palasdinawa , da kuma kungiyar 'yan uwa musulumi ta kasar Masar, muddin tana son a kawo karshen baram-baram din da ita a yankin Gulf.

Ya ce: " Muna so mu ga Qatar ta aiwatar da alkawuran da ta yi a shekarun baya , game da batun tallafawa kungiyoyin 'yan ta'adda, da batun yin katsalandan a harkokin wasu kasashen, da kuma kafafen yada labaranta,'' mun dau wadannan matakai ne cikin matukar bacin rai don tabbatar da cewa Qatar ta fahimci cewa wadannan manufofi ba wadanda za a amince da su bane, kuma dole a sauya su.''

Wannan dambarwa dai ta haifar da nakasu a bangaren farashin danyen mai, da sufurin jiragen ruwa, inda manyan shaguna a Qatar din ke fuskantar matsalar karancin kayayyaki.

Labarai masu alaka