An fara shari'ar wadda ta zuga saurayinta ya kashe kansa

Michelle Carter da saurayinta Conrad Roy Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Ms Carter zuga sauranyinta Mr Roy ya kashe kansa

An gurfanar da wata Ba'amurkiya 'yar shekara 20 wadda saurayinta ya kashe kansa kimanin shekara uku a baya, bayan ta yi ta zuga shi ya hallaka kansa.

Ana tuhumar, Michelle Carter da aikata kisa ba da son ranta ba game da hannun da take da shi a kashe kan Conrad Roy III ya yi wa kansa.

Masu shigar da ƙara sun zargi Misis Michelle Carter da ingiza matashin ɗan shekara 18 daga Massachusetts ya kashe kansa don a taya ta jimami.

Ta dai buƙaci alƙali ya yi mata hukunci amma ba sa'o'inta masu taya alƙali shari'a ba.

A cewar bayanan da Ofishin Lauyan Lardin Bristol ya gabatar Michelle Carter ta aika masa da gajeren saƙon cewa: "Kawai ka yi, Conrad."

"Ka riga ka shirya. Abin da za ka yi kawai shi ne ka kunna jannareto, shi kenan ka rabu da damuwa, ka shiga farin ciki," ta rubuta.

Ta kuma faɗa masa a wani saƙon: "Ƙarshenta dai za ka yi farin ciki a lahira. Ba sauran ƙunci. Ba komai ba ne don ka ji tsoro ai kai ɗan'adam. Ina nufin dai, kwananka ya ƙare."

A lokacin da saurayin yake cikin wasu-wasi, ita kuma ta ƙara tunzura shi.

"Ina tunanin abin da kake so kenan. Lokacin ya yi kuma ka shirya … kawai ka yi rabin raina," ta ƙara cewa.

"Ba saura wani ɗage-ɗagen lokaci. Jira ya ƙare," ta kuma aika masa.

An samu Conrad Roy mace a cikin motarsa sakamakon gubar carbon monoxide a daidai wani filin ajiye motoci na Massachusetts, ranar 13 ga Yulin 2014.

Saƙwannin waya sun nuna kai-komo a shirinsa na ɗaukar ransa a lokacin da ya zauna a cikin motar fikof.

Amma sai Michelle Carter ya ba shi amsa a cikin wani saƙo: "Ka tafi gaba gaɗi."

Bayan mutuwarsa, ta tara gudunmawa don wayar da kai game da batun inganta lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma jagorantar wata gidauniya da ta shirya wasan ƙwallon softball da nufin karrama saurayin nata.

Mahaifiyar matashin, Lynn Roy, ta faɗa wa kotu ranar Talata cewa ba ta samu wani gargaɗi ba game da aniyar Conrad ta kashe kansa.

Ta ce: "Na dai lura yana fama da 'yar damuwa."

A ranar da zai mutu, Conrad Roy ya je gaɓar tekun Westport a Massachusetts, tare da mahaifiyarsa da kuma 'yan'uwansa a cewar masu shigar da ƙara.

Har ma ya saya wa 'yan'uwan nasa askirin, kuma suka yi raha game da tufafin wanka, sun kuma tattauna a kan wani tallafin karatu da ya samu.

Yayin da aka fara muhawara a ranar Talata, an buga saƙwannin waya da suka yi musaya tsakaninsa da Michelle Carter a kotu.

Mataimakiyar Lauyan Lardin, Maryclare Flynn ta ce: "Ta yi amfani da Conrad a matsayin wani karen farauta," ta kuma zargi Michelle da ƙoƙarin son a sani a matsayin wata "budurwar da ke cikin makoki".

Mai shigar da ƙara ta ce: "Ta yi ta ƙoƙarin cire masa duk wata shakka, inda ta ba shi tabbacin cewa iyayensa za su fahimci dalilin da ya sa ya yi hakan, ta binciki dabaru, ta kuma sake ba shi ƙwarin gwiwar cewa zai yi nasara, inda ta ingiza shi har ya daina wata inda-inda, tana zolayar ya cika raki."

Lauyoyi sun buƙaci a kori wannan shari'ah kan hujjar 'yancin da Michelle ke da shi na faɗar albarkacin baki.

Sai dai wani alƙalin kotun matasa ya yanke hanzarin cewa ƙarfafa gwiwar mutum ya kashe kansa ba ya cikin tsarin mulkin Amurka.

Lauyan wadda ake ƙara, Mista Cataldo ya faɗa wa kotu cewa: "Ina taya iyayensa juyayi, amma wannan matashi ne da ya shafe tsawon wata da watanni yana tsara yadda zai kashe kansa".

Labarai masu alaka