Shin ka san amfanin da aure yake da shi wajen kare lafiya?

Burtaniya Hakkin mallakar hoto KUZMICHSTUDIO/GETTY
Image caption Nazarin wanda masana ilmin kimiyya a Burtaniya suka gudanar ya nuna cewa aure, abu ne mai alfanu ga zuciya

Da alamu aure na da matuƙar muhimmanci wajen inganta lafiya, da tsawon rai idan kana da wasu larurori masu alaƙa da ciwon zuciya kamar yadda wasu masu bincike suka gano.

Nazarin wanda masana ilmin kimiyya a Burtaniya suka gudanar ya nuna cewa aure, abu ne mai alfanu ga zuciya.

An shafe tsawon shekara 13 ana gudanar da binciken a kan fiye da mutum dubu 900 masu larurorin da ke da alaƙa da ciwon zuciya, ya gano cewa ma'auratan da ke da yawan maiƙo a jiki sun fi yiwuwar zama a raye da kashi sittin cikin 100 idan an kwatanta da gwagware.

Haka ma labarin yake ga ma'auratan da ke da ciwon suga da hawan jini.

Masu binciken sun yi imani, abokan aure ka iya ƙarfafa gwiwar junansu ta yadda za su ci gaba da zama garau da lafiya. Ko da yake ba su iya tabbatar da hakan ba,

Dr Paul da abokan aikinsa da suka gudanar da wannan bincike, sun riga sun nuna cewa aure na da alaka da samun waraka daga ciwon zuciya.

Binciken baya-bayan nan da aka gabatar a taron ƙungiyar ƙwararru kan cutukan da ke da alaka da bugun zuciya ta Burtaniya, inda ya yi hasashe kan dalilan da ka iya janyo faruwar haka.

Sun yi ittifaƙin cewa aure yakan taimaka wajen kare ma'aurata daga abubuwan da ke haifar da barazanar kamuwa da ciwon zuciya ciki har da maiƙon da ake samu a cikin jini da kuma cutar hawan jini.

A cewar rahoton akwai yiwuwar kashi 16 cikin 100 na maza da mata daga shekara 50, da 60 da 70 masu yawan maiƙon su yi tsawon rai, muddin suka yi aure maimakon zaman gwauronta..

Binciken ya yi tsokaci a kan sabubban mace-macen da ake samu ciki har da ciwon zuciya.

Mata da maza 'yan shekara 50 da 60 da masu 70 da ke da yawan maiƙo na da yiwuwar zama a raye da kashi 16 cikin 100, idan suna da aure maimakon zaman gwauronta, a cewar nazarin.

Haka ma batun yake ga masu ciwon suga da hawan jini, inda ma'aurata ke da damar tsawon rai.

Rahoton dai bai fayyace bayani kan mutanen da ke zaman tare ba aure da waɗanda suka rabu da zawarawa da waɗanda suka saki hannun juna.

Haka kuma, masu binciken ba su gwada ko masu auren suna zaune lafiya cikin farin ciki ba.

Suna ɗauka cewa samun mutumin da ya kwanta ma a rai, ya fi muhimmanci a kan yin auren kawai.

Dr Carter ya ce: "Muna buƙatar ƙara bankaɗo muhimman dalilai, sai dai ga alama akwai wani abu game da yin aure samun kariya, ba kawai ga masu ciwon zuciya ba, har ma ga masu kasadar kamuwa.

"Ba muna cewa ya kamata sai kowa ya yi aure ba ne.

"Muna buƙatar kwatanta alhairan da aure ke da shi ne da kuma amfanin abokai da dangi da sauran rukunonin jama'a masu tallafar mutum a rayuwa."

Dr Mike Knapton, na Gidauniyar kula da lafiyar Zuciya ta Burtaniya, ya ce: "Babban saƙon dai shi ne cuɗanyarmu cikin jama'a, da kuma abubuwan da ke kasada ga lafiya kamar hawan jini muhimman ginshiƙai ne ga lafiyarmu da zama cikin walwala.

"Ko kana da aure ko ba ka da shi, idan kana fuskantar manyan sabubban da kan janyo ciwon zuciya, to ka kira wani abin ƙaunarka don ya taimaka ma."

Sabubban da ka iya lahani ga zuciya:

shan taba

hawan jini

yawan maiƙo a cikin jini

ciwon suga

ƙiba/taiɓa

rashin kataɓus

tarihin ciwon zuciya a dangi

shekaru (ana tsufa kasada na ƙaruwa)

Labarai masu alaka