An yi yajin sayen kayayyakin marmari a Pakistan

A fruit seller takes a nap at a fruit market in Karachi, Pakistan, 26 May 2017. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Farashin kayayyakin marmari sun yi tashi gwauron zabi sakamakon zuwan Ramadan

Masu gwagarmaya a shafukan sada zumunta a Pakistan sun kawo karshen yajin aikin kwanaki uku na kauracewa kayan marmari, saboda su tilasta wa masu sayar da kayan marmari rage fasashin kayayyakin a watan Ramadan.

Ana ganin wannan shi ne karo na farko da masu sayan kayayyakin marmari suka yi amfani da shafukan sada zumunta wajen nuna tsadar kayan abinci a Pakistan.

Wa ke sayen kayayyakin marmarin?

An bayar da rahoton cewa cinikin a manyan biranen kasar ya ragu da kashi 40-50% zuwa ranar Lahadi lokacin da kauracewar ta kare.

Hakan ya tilasta masu saka riba kalilan a kan farashin kayayyakin da suka sayo. Kuma kauracewar a kananan birane da sauran garuruwa ba shi da yawa.

Farashin kayayyakin marmari kan yi tashin gwauron zabi lokacin watan Ramadan, yayin da bukatarsu ke kara karuwa.

A lokacin watan Ramadan dai masu karamin karfi ma na son sayen kayayyakin "masu hali" na marmarin saboda yin buda-baki.

Tuffa, da Ayaba, da kuma Mangoro su ne manyan kayayyakin marmarin da ake amfani da su lokacin watan na Ramadan idan lokacinsu ne.

Me yasa farashin ayaba a fadi?

Riaz Rafi, wani mazaunin birnin Karachi, inda aka kaddamar da yajin, ya ce farashin ya ragu sakamakon yajin aiki.

Ya shaida wa BBC cewa "Ayaba ta sauka daga rufee 100, amma yanzu ta koma zuwa rufee 140.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ayaba ta fadi sanna kuma ta tashi, me ya faru?

Amma Noor Bahadur, wani mai sayar da kayayyakin marmarin a Rawalpindi dake gundumar Islamabad, na ganin faduwar farashi ba shi da alaka da yajin.

"Galibi a watan Ramadan mutane kan yi kokarin sayen kayayyakin, a makon farko ko makonni biyun farko, sai kuma sayen ya dawo yadda aka saba da shi na yau-da-kullum."

"Sweet melon ya fara shigowa, don haka farashinsa na raguwa. Haka kuma mangoro ma ta fara shigowa, don haka ita ma farashinta zai sauka a 'yan kwanaki masu zuwa."

"Amma Ayaba na dab da karewa, don haka farashinta zai ci gaba da tashi duk kuwa da yajin sayen kayan da aka yi."

Ta yaya aka fara yajin sayen?

Kauracewar ta fara ne ta manhajar WhatsApp tun ranar Larabar da ta gabata. Sakon yayi kira ga mutanen Karachi da su kauracewa sayen kayayyakin marmari na kwanaki uku, domin tilasta wa masu sayarwar su rage farashin kayansu.

Daga nan sai kiran ya tsallaka zuwa Facebook da Twitter, in da daruruwan mutane a shafukan sada zumuntan suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu game da kauracewar.

Wa ke da alhakin?

Wani mai sayar da kayayyakin masarufin, mai suna Khalid Nadeem, ya ce kauracewar ba ta yi wani tasiri ba a babban birnin kasar na Islamabad.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu sarin kayakkaykin marmarin sun ce suna tsammanin farashinsu zai ragu da zarar Ramadan ya kama

Ya ce kauracewar za ta yi tasiri ne kawai idan masu sarowa ne suka yi yajin saro kayan daga manyan 'yan kasuwa.

"Kuma kauracewar kwanaki uku ba ta wadatar ba. Za su iya ajiye kayayyakin na tsawon wadannan kwanakin, ba tare da ya shafi ingancinsu ba.

"Kamata ya yi kauracewar ta kai mako guda, ko fiye da haka."

Saura takalma da riguna

Sai dai 'yan kasar na tambayar kansu ko yajin sayen kayan masarufin ya tsaya kan kayayyakin marmari kawai.

Suna ganin ya kamata mutane su kaurace wa sayen tufafi da takalma na musamman masu tsadar da ta wuce misali, saboda bikin Idin Sallah karama a karshen watan na Ramadan.

Labarai masu alaka