Nigeria: An fara biyan masu tona barayin gwamnati

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon yadda EFCC ta gano kudin da ba ta taba gano irinsu ba

A karon farko gwamnatin Najeriya ta biya masu tona asirin barayin gwamnati, inda ta biya mutum 20 naira miliyan 375,875,000.

Kawo yanzu, gwamnatin ta kwato Naira biliyan 11,635,000,000 a sakamakon wannan tsari da aka fito da shi a watan Disamban bara.

Ministar Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta ce: "Wannan shi ne karon farko da muka biya wadannan kudaden a karkashin shirin nan na masu tona asirin barayin gwamnati, kuma yana nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari game da cika alkawurra... ".

Ta kara da cewa "tsarin muhimmin bangare ne na yaki da cin hanci".

Tun farkon shekarar nan, jami'an tsaroa a Najeriya sun bankado makudan kudaden da ake zargin an boye a wurare daban-daban.


Jerin kudaden da aka kwato a baya-bayan nan

  • 3 ga Fabrairu 2017: hukumar EFCC ta gano dala miliyan 9.8 a gidan tsohon shugaban NNPC Andrew Yakubu.
  • 14 ga Maris 2017: Naira miliyan 49 da wani ya gudu ya bari a filin jirgin saman Kaduna.
  • 7 ga Afrilu 2017: Naira miliyan 448 da aka boye a wani shagon canjin kudi dake Victoria Island a Legas.
  • 10 ga Afrilu 2017: Naira miliyan 250 a wani shagon canjin kudade dake kasuwar Balogun a Legas.
  • 11 ga Afrilu 2017: Naira biliyan 4 wanda ake zargin wani dan siyasa daga jihar Neja da sacewa.
  • 12 ga Afrilu 2017: Dalar Amurka miliyan 43 da Naira miliyan 23 da fam 27,000 a wani gida dake Ikoyi a Legas.

A daya bangaren, yakin ya samu koma baya. Hukumar EFCC ta kama wasu mutanen da suka sanar da ita bayanan da basu samar da biyan bukata ba.

Hukumar ta kai farmaki wasu wurare domin gano kudaden da suka ce wai an boye su a wasu wurare. Amma samamen bai samar da komai ba.

A dalilin haka, EFCC ta gurfanar da wasu mutum uku a gaban kotu bisa zargin aikata laifukan bada bayanan karya.

Samamen ya hada da wanda 'yan sanda suka kai gidan mataimakin shugaban majalisar dokokin Najeriya Sanata Ike Ekweremadu, inda basu sami komai ba.

Labarai masu alaka