Nigeria: Gwamna El-Rufai ya sa a kama masu adawa da 'yan Biafra

Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Nasir el-Rufai Hakkin mallakar hoto Kaduna State Government

Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Mallam Nasir El-Rufai, ya bayar da umarnin kame wasu matasa da suka bai wa 'yan kabilar Igbo wa'adin fice wa daga arewacin kasar.

A ranar Talata ne matasan suka shaida wa manema labarai cewa sun gaji da gorace-gorace da gutsuri-tsoma daga kungiyoyin matasan kabilar Igbo masu neman kafa kasar Biafra a kudancin kasar.

Sai dai a wani taron manema labarai, mai magana da yawun gwamna El-Rufai, Samuel Aruwan, ya yi tur da matakin nasu, yana mai cewa "babu wani da zai hana wani zama a duk inda ya so kamar yadda tsarin mulki ya bada dama".

Ya kara da cewa gwamnati ta bayar da umarnin bincike da kama wa da kuma hukunta wadanda suka sa hannu kan sanarwar da matasan suka fitar.

"Gwamnatin Kaduna ta dauki matakin ne saboda matasan sun yi wannan aika-aikar ne a jihar," a cewarsa.

Batun na kafa kasar Biafra dai na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al'ummar kasar, musamman bayan bullar kungiyar matasan Igbo ta IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu.

Kwanan ne wata babbar kotu ta bayar da belin Mista Kanu bayan tsare shi bisa zargin cin amanar kasa.

Yana dai fafutikar ganin an gudanar da kuri'ar raba-gardama ne kan batun kafa kasar ta Biafra.

Gwamnatin Kaduna ta ce idan wasu basu gamsu da wasu abubuwa dake faruwa a wasu jihohi ba, to bai kamata a maimaita irin wannan laifi ba, domin hakan ba shi ne mafita ba.

Ta kuma yin alkawarin kare hakkin duk wani dan Najeriya dake zaune a jihar.

Labarai masu alaka