An ba wa damusa jaki mai rai don yin kalaci da shi

Two tigers play in an enclosure at the Yancheng Safari Park on 28 December 2015. Hakkin mallakar hoto China News Service
Image caption Gidan gandun daji na Yancheng Safari Park na da namun daji sosai

Wata kungiyar masu zuba hannun jari a wani gidan adana gandun daji a China sun fusata, inda suka jefa wa damusa jaki mai rai don su yi kalaci da shi, bayan da suka samu 'yar hatsaniya da hukumar gidan.

Al'amarin ya faru ne a ranar Litinin, a birnin Yancheng da ke lardin Jiansgsu a gaban wadanda suka kawo ziyara gidan.

Gidan adana namun dajin ya ce, masu hannun jarin ne suka jefa wa damusa jakin "cikin tsananin fushi", tare da neman afuwar mutane a kan hakan.

Hotuna da bidiyon al'amarin na ta yawo a shafukan sada zumunta na 'yan kasar, tare da mayar da martani cikin mamaki.

An ga lokacin da aka fito da jakin daga cikin motar daukar kaya, kuma aka shigar da shi wurin da aka kebewa damusar, nan-da-nan kuwa damusa suka daka masa wawa.

An jiyo sautin murya kasa-kasa ta wadanda suka kawo ziyara gidan tare da nuna mamakinsu.

Sai dai a bayanin da aka fitar a shafin sada zumunta na Weibo, gidan adana namun dajin ya ce, hakan ya samo asali ne daga shari'ar da aka yi tsakanin gidan adana namun dajin da wata kungiya.

Wannan matsalar ce ta sa kotu ta rufe asusun bankin gidan adana namun dajin a shekara biyu da ta gabata. Wanda hakan ke nuna cewa ba za su iya sayar da dabbobin ba, kuma "kudin da suke da shi a asusunsu ya yi kasa", in ji su.

Dabbobi da dama, da suka hada da rakumin dawa biyu da gwaggon biri sun mutu, sakamakon gidan adana namun dajin ba sa iya daukarsu a kai su wani wuri domin duba lafiyarsu idan ba su da lafiya.

Jaridar kasar, Xiandai Kuaibao ta ce, bayan da aka jefa jakin, ma'aikatan gidan sun yi kokari wajen hana mutanen shiga garken tumaki.

Gidan adana namun dajin ya ce, wannan al'amari abin "jajantawa ne", kuma za su yi iya kokarinsu wajen tabbatar da cewa, "makamancin haka ba zai kuma faruwa ba".

Labarai masu alaka