Harin Boko Haram a Maiduguri ya sa wasu barin gidajensu

Rundunar Sojin Nijeriya

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY TWITTER

Bayanan hoto,

'Yan Boko Haram din sun kai harin ne a yankin Jiddari Polo dake Maiduguri

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta wargaza wani hari da 'yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram suka kai da maryacen ranar Laraba kan birnin Maiduguri a arewa maso gabashin ƙasar.

Shaidu sun ce amon bindiga ya ɓarke tsawon kimanin sa'a guda.

Harin dai ya faru ne a yankin Jiddari Polo, wata unguwa da ke wajen Maiduguri, a daidai lokacin da mutane ke shirin shan ruwa bayan azumin Ramadan.

Wani mutum daga unguwar Jiddari Polo ya ce al'amarin ya tilasta wa ɗaukacin yankin yin ƙaura zuwa wasu wurare.

Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka dai ya ce haɗin gwiwar sojoji da 'yan sanda sun kashe illahirin maharan ciki har da 'yan ƙunar-baƙin-wake.

Sai dai, ya ce sai nan gaba hukumomi za su ba da cikakken bayani a kan harin.

Al'amarin dai, shi ne wani gagarumin hari na farko da Boko Haram ta kai birnin Maiduguri tun cikin 2016.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran muƙaddashin shugaban Nijeriya, farfesa Yemi Osinbajo zai kai ziyarar aiki birnin Maiduguri ranar Alhamis.