An gargaɗi masu sanƙo game da yankan kai a Mozambique

Mai sanko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu mutane a Mozambique sun yi imani akwai zinare a cikin kan mai sanƙo

'Yan sanda a ƙasar Mozambique sun gargaɗi masu sanƙo cewa matsafa 'yan yankan kai na iya far musu, bayan kisan mutum biyar a baya-bayan nan don cire sassan jikinsu.

An kama mutum biyu da ake zargi a tsakiyar lardin Milange, inda kashe-kashen suka faru.

Kwamandan 'yan sandan lardin Zambezia da ke tsakiyar Mozambique, Afonso Dias ya ce: "Sun yi imani cewa akwai zinare a cikin kan mutumin da ke da sanƙo."

An kakkashe zabiya ma a yankin don yin tsafi da sassan jikinsu.

A cikin makon jiya kaɗai, an kashe mutum uku.

'Yan sanda na jin cewa batun cewa akwai zinare a cikin kan masu sanƙo wata yaudara ce ta bokaye don samun mutanen da za su yanko musu kan irin waɗannan mutane.

An ambato Afonso Dias na cewa "manufarsu ba ta rasa nasaba da camfi da al'adar mutanen yankin da ke zaton mutanen da ke da sanƙo suna kuɗancewa."

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen da ake zargi matasa ne guda biyu 'yan kimanin shekara 20.

Wani mai magana da yawun jami'an tsaron yankin, Miguel Caetano, ya faɗa wa AFP cewa an yanke kan wani mutum kuma aka datse masa al'aura.

Ya ce waɗanda ake zargin sun ce ana amfani da sassan jikin ne wajen yin asiri don samun ƙaruwar arziƙi ga masu kuɗin da ke zuwa neman magani daga Tanzania da Malawi.

A shekarun baya-bayan nan an samu kashe-kashen zabiya a yankin Afirka Ta Gabas, inda bokaye suke amfani da sassan jikinsu don yin asiri.