'Yan gudun hijira miliyan biyu za mu ba tallafin abinci — NEMA

'Yan gudun hijira a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a shafe kwanaki ana aikin raba tan dubu talatin na kayan abinci ga 'yan gudun hijira a jihohin arewa maso gabashin Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta fara wani gagarumin rabon kayan abinci ga 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa kimanin miliyan biyu a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Wannan aiki, wanda jami'ai suka ce ba a taɓa yin irinsa ba, zai shafe tsawon kwanaki ana aiwatarwa, inda za a raba tan dubu talatin na kayan abinci iri daban-daban.

An shafe tsawon lokaci ana ƙorafin cewa mutanen da rikicin na Boko Haram ya shafa ba sa samun kulawar da ta kamata.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA ce za ta jagoranci wannan gagarumin aiki.

Shugaban hukumar, Injiniya Mustafa Yunusa Maihaja, ya yi wa BBC karin bayanin cewa gwamnati ta ji kukan da suka gabatar mata, inda ta tanadi kayan abinci iri daban-daban sama da tan dubu talatin don kai wa jihohin da rikicin Boko Haram ya fi shafa.

Jihohin sun hadar da Borno da Adamawa da Taraba da Yobe da kuma Bauchi.

Manyan motocin ɗaukar kaya kimanin dubu ɗaya da talatin da ɗaya ne za su ɗebi buhunan abincin daga rumbunan gwamnati zuwa waɗannan jihohi.

Zarge-zargenkarkatar da tallafi

A duk lokacin da aka yi maganar raba kayan abinci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, a kan samu korafe-korafen cewa ba sa isa wurin mutanen da aka tanada dominsu.

Amma kuma shugaban hukumar ta NEMA ya ce a wannan karon an yi tanade-tanade irin wanda dokar kasa da kasa ta tanada cewa a bayar da isasshen abinci ga 'yan gudun hijira.

Ya kara da cewa: '' A tsari dai ana la'akari da cewa a ko wane gida akwai mutane shidda ne,'' don haka ko wane gida za a bayar da kilo hamsin da digo hudu na abinci abinci daban-daban.''

Injiniya Mustapha ya kuma ce 'yan gudun hijirar da ke sansanoni, da wadanda ba a sansanoni suke ba duk za su amfana da wannan tallafi na abinci.

Kana ya ce : '' Gaskiyar magana ma duk wani wanda ya ajiye 'yan gudun hijira a gidansa zai amafana da wannan tallafi.''

Hukumar ta NEMA ta kuma ce ta riga ta kammala aikin tantance yawan 'yan gudun hijirar, da kuma inda suke, da kuma yadda za a rarraba musu tallafin kayan abincin.

Labarai masu alaka