Iran ta zargi Saudiyya da Amurka a harin da aka kai mata

Jami'an tsaro na sintiri a birni Tehran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bayan shafe sa'oi ana barin wuta a kusa da majalisar dokokin Iran, mahukunta sun ce duka maharan sun mutu

Askarawan juyin-juya-halin ƙasar Iran sun zargi ƙasashen Saudiyya da Amurka da hannu a harin da aka kai wa majalisar dokokin ƙasar da kuma hubbaren jagoran juyin-juya-halin Iran Ayatollah Khomeini.

Kasar Saudiyya ta musanta zargin hannu kan duk wani abu da ya shafi harin da ƙungiyar IS ta ce ita ke da alhakin kai wa.

Da yake taya alhininsa kan mutum 12 da suka mutu a harin, shugaban Amurka Donald Trump, ya yi kashedin cewa duk ƙasar da ke mara wa ta'addanci baya, ita ma za ta faɗa cikin hatsarin ta'asar 'yan ta'addan.

Ƙasar Iran din ta ce maharan da suka hallaka mutum 12 tare da jikkata wasu da dama a Tehran babban birnin kasar Iraniyawa ne da suka shiga ƙungiyar IS da ke kiran kanta daular musulunci.

Yan harin ƙunar-bakin-wake ne dai suka kai hari a ginin majalisar dokoki da kuma a hubbaren jagoran juyin-juya-halin Islama na Iran Ayatollah Khomeini.

Kungiyar IS ta ce ita ce ke da alhakin kai harin, ta kuma yi barazanar cewa wannan shi ne mafarin hare haren da za ta rika kai wa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai kai hare haren.

Duka maharan dai sun mutu, yayin da aka cafke wasu mutum biyar da aka yi amanna suna shirin kai hari na uku, in ji hukumomi.

Hakan na zuwa ne yayin da ake fuskantar rashin jituwa a yankin gabas ta tsakiya, bayan Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa sun yanke hulda da kasar Qatar kan zargin tallafawa masu tsattauran ra'ayin addini da kuma kusancinta da kasar Iran.

A wata hira da gidan talabijin na kasar, mukaddashin majalisar koli ta tsaron Iran din, Reza Seifollahi, ya ce maharan sun shiga kungiyar I-S daga sassa bda dama na kasar:

" Harin ta'addancin ya faru ne mako guda bayan ganawar shugaban Amurka da kuma takwaransa na kasar Saudi Arabia..hakan ya nuna cewa akwai kanshin gaskiyar cewa suna da hannu a wannan hari,''

Dama dai ba a ga maciji da juna tsakanin kasar Saudi Arabia mai bin tafarkin Sunni,da kasar ta Iran wacce akasari 'yan Shi'a ne.