An gano wasu baraguzan jirgin Burma da ya yi batan dabo.

A Myanmar Air Force Shaanxi Y-8 transport aircraft being unloaded at Sittwe airport in Rakhine state, of the same type as the plane that is missing (file photo) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin saman sojin Burmar kirar Y-8

Sojin Burma sun ce, an tsinci gawawwaki da kuma wasu tarkace, bayan da jirgin sojin kasar ya yi batan dabo da mutum 122.

Sojin sun bayyana a shafinsu na Facebook cewa, an gano tarkacen a tarwatse a cikin tekun Andama.

Jirgin kirar Y-8 da aka kera a kasar China, yana dauke da ma'aikata 14. Yawancin fasinjojin da suke ciki sojoji ne da kuma iyalansu, wadanda suka hada da yara.

An daina jin duriyar jirgin ne ranar Laraba, bayan sa'a daya da rabi da tashinsa.

A cewar sojin, jami'an da suke aikin nemo shi ne suka gano gawa 10 a safiyar Alhamis, wadanda suka hada da yara, da wasu kayayyaki, da rigunan ceton rai na cikin jirgi. Sai dai har yanzu ba a gano manyan sassan jirgin ba.

Idan dai har duk wadanda suke cikin jirgin sun mutu, hadarin zai zama mafi muni da kasar ta taba fuskanta a banagren jiragen sama.

Har yanzu ba a san dalilin hatsarin ba. kuma ba a samu wani rahoto da yake nuna cewa matukin ya bukaci agajin gaggawa, ko wani bayani kan yadda al'amarin ya faru a sararin samaniya ba.

A cewar sojojin, an sayi jirgin ne daga kasar China a watan mayun bara, kuma ya yi tafiyar sa'a 809.

Karin bayani