Kungiyar Al-shabab ta kai hari sansanin Sojin Somalia

Al-Shabab Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Al-Shabab dai na kaddamar da hare-hare a kan sansanonin soji a Somaliya

Kungiyar Al-shabab ta kaddamar da wani babbab hari kan wani sansanin soji a yankin Puntland mai kwarya-kwaryar cin gashin kansa.

Kungiyar ta ce mayakanta sun kashe sojojin gwamnati 61, sun kuma kwace motoci 16 a harin da suka kaddamar da asubahin ranar Alhamis.

To sai dai wani minista a gundumar ta Puntland ya musanta wannan ikirarin na yawan mutanen da aka kashe, amma kuma bai bayar da cikakken bayani ba game da yawan wadanda suka jikkata a harin ba.

Kungiyar wacce ke da alaka da kungiyar al-Qaeda na kaddamar da hare-hare da dama a barikokin sojin Somaliya.

Ko a watan Janairu ma, kungiyar ta ce ta kashe sojojin Kenya 50 a wani hari da ta kaddamar kan wani sansanin sojin dake garin Kolbiyow dake kudancin kasar.

Sojojin Kenya dai na cikin dakarun kawancen Afirka 18,000, dake taimaka wa gwamnati wajen yakar al-shabab a Somaliya.

Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa maharan sun fice daga cikin garin bayan sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta da sojojin gwamnati.

Da yake tabbatar da harin, ministan tsaro na yankin na Puntland Abdiaziz Hirsi ya ce ana kan gudanar da bincike, kuma za a ji karin bayani nan gaba.

Tsaunukan Galgala dai nan ce babbar tungar kungiyar ta al-Shabab, sai dai wani bangare na kungiyar ya ware a shekarar 2015 inda ya yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Labarai masu alaka