Nigeria: "Mutum '13' ne suka mutu a harin Maiduguri"

Sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kashe mutum 14 a harin Boko Haram a Maiduguri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce harin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a garin Maiduguri dake jihar Borno a lokacin buda-baki ya kashe mutum 13.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Victor Osoku ya shedawa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kashe fararen hula 10, yayin da uku daga maharan suka mutu.

Haka kuma Victor ya ce mutum 24 sun jikkata a harin.

Ya kara da cewa an kama wani da ake zargi dan Boko Haram ne da ransa

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno Damian Chukwu ya shedawa wani taron manema labarai a birnin Maiduguri cewa, 'yan Boko Haram din sun yi amfani da bindigogin kakkabo jirgi yayin harin da aka kai ranar Laraba.

A wata hira da BBC, kakakin rundunar sojan Najeriya Birgediya Sani Usman Kuka-Sheka, ya ce an kashe gaba-daya 'yan Boko Haram din da suka kai harin.

Harin dai ya faru ne a yankin Jiddari Polo, wata unguwa da ke wajen Maiduguri, a daidai lokacin da mutane ke shirin buda-baki

Mazauna yankin sun ce amon bindigogi ya ɓarke har tsawon kimanin sa'a guda.

Wani mutum daga unguwar Jiddari Polo ya ce al'amarin ya tilasta wa ɗaukacin mazauna yankin yin ƙaura zuwa wasu wurare.

Labarai masu alaka

Karin bayani