Masu zuwa Qatar domin aiki sun shiga damuwa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Masu zuwa Qatar domin aiki sun shiga damuwa

Qatar ce ke da darajar arzikin da ake samarwa a cikin kasa GDP mafi girma a duniya, wanda kuma daruruwan ma'aikata baki daga kasashe 80 ke taimakawa wajen bunkasarsa. A yanzu bakin suna zaman dar-dar sabo da takkadamar diplomasiyya da ta kunno kai tsakanin kasar da wasu kasashe na yankin tekun Fasha.