Al-Shabab ta kashe dakaru 61 a Puntland

Harin kungiyar al-Shabab Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harin al-Shabab a Puntland

Kungiyar al-Shabab a Somaliya ta sanar da cewa ta kashe dakarun gwamnati 61 a yankin Puntland mai kwarya-kwaryar 'yancin kai a wani hari mafi girma da ta kai.

Ta kumayi awon gaba da motoci 16 a lokacin harin.

To sai dai ministan tsaro a gwamnatin ta Puntland, Abdlaziz Hirsi ya masunta yawan dakarun da kungiyar ta ce ta kashe ba tare da ya bayar da yawan wadanda suka mutun ba. Ya kara da cewa ana cikin gudanar da bincike kan lamarin.

al-Shabab mai alaka da al-Qaeda ta sha kai hare-hare sau da dama a cibiyoyin dakarun kasar Somalia.

Labarai masu alaka