Birtaniya: Theresa May ta kasa samun rinjaye

kidayar kuri'u Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Duk jam'iyyar da ta samu kujerun majalisar dokoki 326 cikin 650 da ake da su a kasar, ita ce za ta kafa gwamnati

Firai Ministar Birtaniya Theresa May ta rasa samun rinjayen da take bukata don kama gwamnati bayan samun sakamakon da yawa daga cikin kujerun majalisar dokokin Birtaniya.

Jam'iyyar da ta samu kujerun majalisar dokoki 326 cikin 650 da ake da su a kasar, ne za ta kafa gwamnati.

Ana ganin Jam'iyyar Conservative mai mulki tana kan gaba, amma kuma da wuya ta samu rinjayen da ake bukata da zai ba ta damar kafa gwamnati.

Idan ba a samu jam'iyya daya da ta samu rinjayen da ake bukata ba, to jam'iyyar da ta fi samun yawan kuri'u a zaben za ta kulla hadaka da karamar jam'iyya don su kafa gwamnati tare.

Sai dai ga alama wannan sakamakon ba zai yi wa Misis May dadi ba, saboda yadda ita ce bisa radin kanta ta kira zaben na ba zata a tunanin za ta samu gagarumin rinjaye, amma sai gashi reshe yana so ya juye da mujiya.

An rufe rumfunan zaɓe da misalin karfe 10 na dare kuma an fara ƙidaya ƙuri'u a Birtaniya.

An bude rumfunar da zabe ne da misalin karfe 7 na safe a ranar Alhamis kuma mutane kimanin miliyan 46 ne suka kada ƙuri'unsu daga Ingila da Scotland da Wales da kuma Northern Ireland. Kuma Jam'iyyu bakwai ne suke fafatawa a zaben.

Nick Clegg ya faɗi a mazaɓarsa

Tsohon Mataimakin Farai Ministan Birtaniya Nick Clegg ya sha kayi a hannun dan jam'iyyar Labour a mazabar Sheffied Hallam.

Alex Salmond ya faɗi a mazaɓarsa

Hakazalika, tsohon Shugaban jam'iyyar Scotish National Party Alex Salmond ya sha kayi a mazabarsa ta Gordon.

Jim kadan bayan fara bayyana hasashen sakamakon zaben ne, darajar kudin kasar wato fam ya fadi idan aka kwatantashi da na dalar Amurka.

A watan Afrilu ne Farayi Ministar Birtaniya,Theresa May ta ba da sanarwar kiran zaben ba zata.

Misis May ta ce Britaniya na bukatar yanayi na tabbas da zaman lafiya da shugabanci mai dorewa bayan zaben raba gardamar ficewa daga Tarayyar Turai da aka yi a bara.

Labarai masu alaka