Mene ne tasirin zaɓen Birtaniya ga ƙasashen Afirka?

Zaben Birtaniya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Birtaniya ce ta yi wa ƙasashen Afirka da dama mulkin mallaka

A ranar Alhamis ne jama'a kasar Birtaniya suka je rumfunar zaɓe don kaɗa ƙuri'unsu a babban zaɓen ƙasar.

Zaɓen zai fi zafi ne tsakanin 'yan takara biyu wato Firai Minista Theresa May ta jam'iyyar Conservative da kuma Shugaban Jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn.

Cikinsu duk wanda ya samu nasara sakamakon yana da tasiri sosai ga kasashen Afirka.

Ƙasar Birtaniya ta yi wa wasu ƙasashen Afirka mulkin mallaka kuma gallibinsu mambobi ne a Ƙungiyar Ƙasashe Renon Birtaniya wato Common Wealth.

A bara ne ƙasar ta zaɓi ficewa daga Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).

Jakadan Burtaniya a EU ya yi murabus

Theresa May ta bukaci a gudanar da zaben ba zata

Bayan batun tsaro, batun EU ana ganin shi zai taka muhimmiyar rawa a zaɓen musamman idan ana maganar makomar ƙasar.

Akwai masana da suke cewa duk wanda ya samu nasara a zaɓen, zai sake waiwayon dangantakar ƙasar da nahiyar Afirka musamman ta yadda za a ƙulla sabuwar yarjejeniyar cinikayya da kasuwanci bayan ficewar ƙasar daga EU, ta amfani da ƙungiyar Common Wealth.

Hakazalika ta fuskar tsaro. Akwai masana da suke ganin ƙasashen Afirka suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen taimakawa ƙasar shawo kan tsaron cikin gida, musamman hare-haren da masu iƙirarin kishin addini suke kai mata a 'yan kwanakin nan.

A ƙarshe akwai magana ƙaurar jama'a wato yadda mutanen Afirka suke tafiya ci rani can. Har ila yau, akwai kuma batun mutanen Afirka da dama da suke zaune a Birtaniya. Akwai kimanin 'yan Afirka miliyan ɗaya da suke zaune a can.

Manufofin wanda ya lashe zaɓen ka iya shafar 'yan Afirka da suke Birtaniya, da kuma wadanda suka dogara da su da suke zaune a gida Afirka da ma wata ƙila nahiyar baki ɗaya.

Labarai masu alaka