Theresa May ta ci kujerar mazaɓarta

Farai Ministan Birtaniya Hakkin mallakar hoto Getty Images.

Farai Ministar Birtaniya Theresa May ta jam'iyyar Conservative ta lashe kujerar mazaɓarta ta Maidenhead.

Hakazalika, Shugaban Babbar Jam'iyyar adawar kasar wato Labour, Jeremy Corbyn, shi ma ya lashe kujerar mazaɓarsa ta Islington North.

Sai dai a jawabin da ya yi, Mista Corbyn ya bukaci firai ministar da ta yi murabus "don ta bayar damar kafa gwamnati wadda za ta kasance ta wakilan jama'ar kasar ne na zahiri."

Ya ce kawo yanzu yana "alfahari da sakamakon" wanda ya ce sakamako ne da ke "nuni da kyaykyawar makoma" kuma ya ce mutane "sun fara kin goyon bayan matakan tsuke bakin aljihu".

Sai dai Misis May ta ce wannan lokaci ne da ke bukatar zaman lafiya.

Ta ce idan da a ce jam'iyyar Conservative ta lashe galibin kujerun da kuri'un "'to wajibi ne a gare mu mu tabbatar da zaman lafiya kuma wannan shi ne abin da za mu yi".

Har ila yau, ta ce duk abin ta yi ta yi shi ne don ci gaban kasar.

Ana hasashen cewa Jam'iyyar Conservative mai mulki za ta yi galaba, amma kuma da wuya ta samu rinjayen da ake bukata da zai ba ta damar kafa gwamnati ita kadai, sai ta kulla hadaka da kramar jam'iyya don su kafa gwamnati tare.

Sai dai ga alama wannan sakamakon ba zai yi wa Misis May dadi ba, saboda yadda ita ce ta kira zaben na ba zata a tunanin za ta samu gagarumin rinjaye, amma sai reshe yake so ya juye da mujiya.

Labarai masu alaka