James Comey ya ce gwamnatin Trump ta zambaɗa mai ƙarya

James Comey Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Comey ya zargi shugaba Trump da yunƙurin mayar da shi ɗan amshin shata.

Tsohon daraktan hukumar tsaron Amurka, FBI, James Comey ya faɗa wa zaman Majalisar ƙasar cewa kalaman gwamnatin Trump a game da shi da da kuma hukumar FBI "ƙarairayi ne tsagwaro".

Mista Comey ya faɗa wa kwamitin Majalisar Dattijai cewa ba su yi daidai ba da suka ƙasƙantar hukumar da kuma shugabancinsa.

Ya kuma shiga "ruɗani" da "sauya maganar" da aka yi kan sallamarsa, da ta zo a lokacin da ya jagoranci bincike kan wata alaƙa tsakanin ayarin yaƙin neman zaɓen Trump da Rasha.

Daga bisani shugaba Donald Trump ya ce bai taɓa neman kawo cikas a binciken ba.

Lauyan Mr Trump, Marc Kasowitz, ya faɗa a wata sanarwa cewa shaidar James Comey "a ƙarshe dai ya tabbatar a bainar jama'a" cewa ba a binciken shugaban da hannu a katsalandan Rasha cikin harkokin siyasar Amurka.

A cikin sanarwar, Mista Trump ya kuma musanta tuntuɓar Comey don ya yi masa biyayya ko ya watsar da binciken da ake yi wa mashawarcin tsaron Amurka da aka sallama daga aiki, Michael Flynn a lokacin haɗuwar da suka sha yi.

A shaidar da ya bayar, Mista Comey ya ce Donald Trump ya sha faɗa masa cewa aikinsa yana "kyau".

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaman kwamitin binciken Majalisar Dattijan Amurka

Ya kuma nunar cewa an kore shi daga aiki ne don "sauya yadda ake gudanar da bincike game da katsalandan ɗin Rasha".

Tsohon shugaban FBI, akasari ya kasance cike da nutsuwa a kusan shaidar tsawon sa'a uku da ya gabatar, ko da yake, shauƙi ya dabaibaye shi lokacin da yake gabatar da jawabinsa na buɗewa.

Ya faɗa wa ayarin masu binciken cewa fadar White House ta "so ɓata min suna, da kuma uwa-uba kuma hukumar FBI, inda ta yi iƙirarin "raunin jagoranci," a hukumar.

"Waɗannan ƙarairayi ne, ba daɗi ba ragi. Na kuma yi takaicin cewa ma'aikatan FBI sai sun bi abin da suka ce," in ji shi.

"Hukumar FBI mai gaskiya ce. FBI na da ƙarfin hali. Kuma FBI na da 'yancin cin gashin kanta kuma a ko da yaushe haka za ta kasance," ya faɗa a jawabansa na buɗewa.

Mista Comey na jagorantar ɗaya daga cikin bincike-binciken da ake yi game da hulɗa da Rasha kafin a kore shi daga aiki.

Hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi imani Rasha ta tsoma baki cikin harkokin zaɓen Amurka, kuma suna binciken zargin alaƙa tsakanin ayarin yaƙin neman zaɓen Trump da hukumomin birnin Moscow.

Sai dai, babu wata sananniyar shaida kan wani haɗin baki kuma Shugaba Donald Trump ya yi watsi da batun a matsayin "labarin ƙanzon kurege".

Mai magana da yawun shugaban Sarah Sanders a ranar Alhamis ta mayar wa Mista Comey martani a, inda ta ce: "Zan iya rantsuwa shugaban ƙasa ba maƙaryaci ba ne."

Labarai masu alaka