Nigeria ta ce ta duƙufa don kafa matatar mai a Katsina

Matatar mai a Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana son ganin kowacce shiyya ta Nijeriya ta samu matatar mai don samun wadatarsa, in ji hukumomi.

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta duƙufa wajen kafa matatar man fetur a jihar Katsina, ta yadda ƙasar za ta samu ƙarfin tace man da ake buƙata har ma da na ƙasashe maƙwabta.

Matakin wani yunƙuri ne na ƙara adadin matatun man fetur a Nijeriya da kuma gyara waɗanda ake da su don ƙasar ta iya dogara da kanta.

Malam Umar Faruk babban jami'i mai kula da ayyuka na musamman ga ministan albarkatun man fetur na Nijeriya ya ce ko da yake, Nijeriya a yanzu ba ta da kuɗin da za ta gyara illahirin matatun ƙasar, amma ta duƙufa wajen nemo masu zuba jari da za su sanya dukiyarsu a wannan aiki.

Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta ƙuduri aniyar kafa matatar mai a duk shiyyoyin ƙasar shida, don tabbatar da wadatarsa.

Umar Faruk ya ce kafa matatar man fetur a Katsina zai ba wa Nijeriya damar tallafawa wajen tace man da jamhuriyar Nijar take haƙowa a ƙasarta.

Ya ce Nijeriya na gudanar da tuntuɓa da masu sha'awar zuba jari don ganin yadda za a farfaɗo da matatun man ƙasar.

"Ba wai za su zo da kuɗi ne a sayar musu da matatun ba, za su zo a haɗa gwiwa a yi wannan gyara ta yadda matatun za su kai matsayin da za su rika aiki (gadan-gadan).'

Ya kuma ce kamar yadda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni na tabbatar da gyara ɗaukacin matatun mai na ƙasar, ministan man fetur Mista Ibe Kachukwu ya ɓullo da tsare- tsaren nemo masu zuba jarin da za a haɗa hannu da gwamnati.

A cewarsa hakan ba yana nufin gwamnati na da niyyar sayar da matatun mai na kasar ba.

A baya dai an ambato Ibe kachukwu na cewa rashin tsare-tsare da za a daɗe ana cin gajiyarsu ne ya kawo taɓarɓarewar al'amura a ɓangaren samar da man fetur na Nijeriya.

Labarai masu alaka