Birtaniya: Theresa May za ta nemi kafa sabuwar gwamnati

Babu jam'iyyar da ta samu rinjaye a zaben Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Zaben na Birtaniya ya rikitawa jam'iyyar Conservative lissafi

Theresa may za ta ziyarci fadar sarauniyar Ingila da karfe 12:30 na rana ,domin neman izinin kafa sabuwar gwamnatin Burtaniya, duk kuwa da rasa rinjaye da jam'iyyarta Conservative ta yi a zaben majalisar kasar da aka gudanar ranar Alhamis.

Tana neman ci gaba da kasancewa Farayiminsta ne, bayan ta fahimci cewa jam'iyyar DUP ta Ireland ta arewa za ta goyi bayan May ta kafa gwamnatin 'yan tsiraru.

Jam'iyyar Conservative dai ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar Burtaniya bayan ta yi asarar kujeru takwas.

Tuni Jeremy Corbyn ya yi kira ga Theresa May ta yi murabus, inda ya ce jam'iyyar Labour a shirye take ta karbi jagoranci.

Idan an hada kujerun Conservative da na DUP dai za su kujeru 329 a majalisar dokokin,

Theresa May dai ta nuna aniyarta ta neman kafa sabuwar gwamnati, inda tace kasar na bukatar sanin ind ata sa gaba, kwanaki 10 gabanin a fara tattaunawar kasar daga tarayyar turai.

Har yanzu dai jam'iyyar DUP ba ta fito fili ta bayyana aniyarta ta yin hadaka da jam'iyyar Conservative ba, amma dai alamu na nuna cewa tuni ta yanke hukuncin yin hakan.

Jami'yyar Conservative dai ta samu kujeru 318, yayin da abokiyar hamayyarta Labour ta samu kujeru 261 a zaben da aka gudanar ranar Alhamis.

Karin bayani