An zabi Preet Gill a mace ta farko mai bin addinin Sikh zuwa majalisar Burtaniya

Preet Gill
Image caption Zaben Burtaniya 2017: Preet Gill ce mace 'yar Sikh ta farko aka zaba zuwa majalisa

An zabi mace ta farko mai bin addinin Sikh zuwa majalisar Burtaniya.

Preet Gill ta sami kuri'u 24,124 wanda ya bata daman lashe zaben mazabar Birmingham Edgbaston a karkashin jam'iyyar adawa ta Labour da ratar kuri'u 6,917.

Gisela Stuart ce a da take wakiltar mazabar, amma ta fasa tsayawa takara a lokacin da aka bayyana za a yi zaben.

Ms Gill tace, "Abin girmamawa ne, a ce ni ce zan wakilci jama'ar mazabar da aka haife ni kuma na tashi a cikinta." Ta ce batun ilimi shi ne babban abin da zata fi maida hankalinta a kai.

Birtaniya: Theresa May na fuskantar matsin lamba

Mene ne tasirin zaɓen Birtaniya ga ƙasashen Afirka?

"Mun yi yakin neman zabe mai inganci, kuma mun yi sa'ar samun mutanen kirki da suka taimaka mana a nan Edgbaston, wannan abin alfahari ne."

Ta kara: "Ina farin cikin samun damar wakiltar jama'ar wannan yankin, kuma ina sa ran saduwa da su", in ji ta.

'Abar koyi'

Bhai Amrik Singh shi ne shugaban babbar hadakar 'yan Sikh, ya ce: "Muna murnar samun mace ta farko mabiya addinin Sikh wacce ta zama 'yar majalisar Burtaniya, watau Preet Kaur Gill a Birmingham, ta mazabar Edgbaston.

"Zata kasance 'yar majalisa abar alfahari ga al'ummar Sikh kuma abar koyi."

Caroline Squire, wacce 'yar jam'iyyar Conservative ce tazo ta biyu a bayan Preet Gill da kuri'u 17,207.

Shi kuma dan jam'iyyar Lib Dem watau Colin Green yazo na uku da kuri'u 1,564, kana Alice Kiff ta jam'iyyar Green ta samu kuri'u 562, shi kuma Dick Rodgers na jam'iyyar Common Good ya sami kuri'u 155.

Karin bayani