Hotuna daga Afirka a wannan makon: 2 ga Yuni - 8 ga Yuni 2017

Zababbun hotuna masu kayatarwa daga sassa daban-daban na Afirka da ma wasu sassa na duniya a makon nan.

asu tallata kayan sanyawa suna jira su fito wajen nuna kaya a bikin na birnin Legas ranar 3 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tallata kayan sanyawa suna jira a lokacin bikin Makon Kayan Sawa na Afirka a Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, ranar Lahadi.
Masu tallata kayan sanyawa suna jira su fito wajen nuna kayan da Nkem, wacce 'yar Najeriya ce mai shekaru 13 da haihuwa a wurin bikin a birnin Legas ranar 3 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bikin na tallata kayayyakin sanyawa mafi kayatarwa daga kasashen Najeriya, Senegal, Kamaru, Ghana da Zambiya.
Wannan tsuntsun macaw din an ganshi ne a gidan killace dabbobi a kan hanyar hamada ta Al-Kahira zuwa Iskandariyya ranar 7 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ranar Alhamis a Masar an ga wani tsuntsu, mai suna macaw, nau'in aku kuturu a wani gidan killace dabbobi a kan hanyar Al-Kahira zuwa Iskandariyya.
Wasu wadanda ambaliyar ruwa ta kore su daga muhallansu suna kokarin kwashe kayansu a garin Nyala dake wilayar Darfur ta Kudu a Sudan ranar 3 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Su kuma a yankin Darfur na kasar Sudan, wasu mutane ne ke kaura daga gidajensu bayan ruwan sama mai yawa da ya fadi ranar Lahadi.
Wani mutum na guje wa feshin ruwan teku a Cape Town Afirka ta Kudu ranar 7 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai daukan hoto ya jajirce domin daukan hoton wata guguwar iska da ruwa a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
Wani mutum na daukan hoton feshin ruwan teku a Cape Town Afirka ta Kudu ranar 7 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne yanayin hunturu mafi muni a cikin shekaru 30 da suka gabata a birnin na Cape Town.
Mawakan kungiyar El Hadhra suna rera wakokin yabo a lokacin bikin a dakin wasanni na La Medina na birnin Tunis ranar 6 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ranar Talata a birnin Tunis, wasu mawaka sun yi wani wasa a lokacin wani biki.
Mawakan kungiyar El Hadhra suna rera wakokin yabo a lokacin bikin a dakin wasanni na La Medina na birnin Tunis ranar 6 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana gabatar da bikin a kowace shekara a daidai watan Ramadan, kuma bikin na Sufaye ne.
Wata mata zabiya na jiran abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira kusa da Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya ranar 6 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A arewa maso gabashin Najeriya, wata mata ta na jiran ta karbi abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira kusa da Maiduguri.
Wata yarinya ke wucewa cikin wasu runfunan wucin gadi a sansanin 'yan gudun hijira a wajen birnin Maiduguri, arewa maso gabashin Najeriya ranar 6 ga watan Yuni 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tana cikin dubban mutanen da suke kakewa a sansanin domin neman kariya daga hare-haren kungiyar Boko Haram.
Shugaba Robert Mugabe (hagu) da matarsa Grace (dama) suna murmushi a wajen taron siyasa a filin wasa na Rudhaka na birnin Marondera misalin kilomita 100 gabas da Harare Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Jumma'a, shugaba Robert Mugabe da matarsa Grace sun halarci wani gangamin siyasa a gabashin garin Marondera.
Magoya bayan shugaba Mugabe a garin Marondera suna hartar gangamin zabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan yana cikin jerin tarurrukan siyasa da Mista Mugaben mai shekaru 93 ke halarta domin neman goyon bayan jama'a gabanin zaben shugaban kasa na badi.
Masu goyon bayan shugaba Mugabe ke nan a wajen taron siyasa a Marondera Zimbabwe. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tarukan gangamin na neman jawo hankalin matasa ne amma wannan bai hana wasu matasan dattawa halarta ba.

An samo hotunan daga AFP, EPA, Getty Images da Reuters

Labaran BBC