Zaben Birtaniya: Kasashen duniya sun maida martani

Firayi Ministar Burtaniya Theresa May tan barin ofishin jam'iyyar Conservative bayan zaben Burtaniya a Landan ranar 9 ga watan Yuni 2017 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayi Ministar Burtaniya Theresa May na fuskantar kiraye-kirayen ta yi murabus

Shan-kayen da jam'iyyar Conservative tayi, wanda ya janyo mata rashin rinjaye a zaben Birtaniya ya gigita Turai da sauran sassan duniya.

'Yan siyasa daga nahiyar Turan sun fara duba tasirin zaben a kan tattaunar da za a yi da Burtaniya kan ficewarta daga Turai.

Shugaban knugiyar ta tarayyar turai, Jean-Claude Juncker ya ce yana so a fara tattaunawar ba tare da bata lokaci ba.

"A namu bangaren, muna kallon yadda zamu fara tattaunawar gobe da misalin karfe tara da rabi", in ji shi.

Firayi Ministan Carl Bildt, wanda shi ke shugabancin kwamitin sa ido na harkoki da kasashen waje na Tarayyar Turai ya kira zaben "yamutsi".

"Wani yamutsin na iya biyo wannan yamutsin. Abin da rashin jagoranci na gaskiya ke haifarwa ke nan", ya wallafa a Twitter.

'An sake cin gida'

Guy Verhofstadtwanda shi ne shugaban hadakar 'yan siyasa masu sassauci a majalisar Tarayyar Turai bai yi watat-wata ba wajen kushe Misis May da kakkausar murya.

"Wannan ai kamar dan kwallo ne ya sake cin gidansu, bayan Cameron yayi nasa, yanzu kuma ga May, wannan zai kara rikirkita tattaunawar da dama rikirkitacciya ce", shi ma ya wallafa a Twitter.

Shi ko Michel Barnier wanda shi ne babban mai shiga tsakani a tattaunawar ta Brexit, yayi kalamai masu kwantar da hankali. "Ya kamata a fara tattaunawar batun ficewar Birtaniya a lokacin da kasar ta shirya.

Karin bayani