An sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Batun sace mutane dan neman kudin fansa na ci gaba da zama barazana a Najeriya
Image caption Gwamna Nasiru El-Rufa'i ya sha alwashin magance matsalar

An karbo uku daga cikin mutum 20 da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja da ke arewacin Najeriya.

Wani dan asalin jihar Kaduna mai suna Kwamared Danjuma Sarki, wanda ya wallafa sace wasu abokansa a shafukan sada zumunta da muhawara, ya shaida wa BBC cewa ya karbo mutane ne bayan ya bayar da kudin fansa.

''Sun bukaci kudin fansa, na kuma kai musu; ba su sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su ba, don haka mutum uku kadai suka ba ni'', in ji Danjuma.

Sai dai bai bayyana adadin kudin da ya bayar kafin a saki mutanen ba.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta sace mutum 20 a hanyar Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Usman ya gaya wa BBC cewa "babu wani rahoto mai kama da wannan da 'yan uwa ko wasu mazauna yankin suka kai wa jami'an tsaro kamar yadda aka saba a baya".

A cewarsa, mutum biyar kawai suka samu labarin an sace a hanyar.

'Dan majalisa ya fada hannu'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokuta da dama wadanda aka yi garkuwa da su kan rasa rayukansu idan aka taki rashin sa'a

Jama'a a yankin birnin Gwari na jihar Kaduna ma na ci gaba da zaman dar-dar, saboda sake dawowa dauki dai-dai din da ake yi musu.

Wani mazaunin birnin Gwari ya shaida wa BBC cewa an sace wani dan majalisar dokokin jihar ranar Alhamis.

Ya zargi masu satar shanu da hannu a sace-sacen mutanen, yana mai cewa ''Kamata ya yi gwamnati ta tilastawa masu satar shanu da aka yi wa ahuwa su kawo makamansu kamar yadda aka yi a jihohin Katsina da Zamfara, ba wai a bar su da su a hannu su yi yadda suka ga dama ba''.

A shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta lashi takobin kawo karshen satar shanu da garkuwa da mutane da jihar ke fama da su.

Labarai masu alaka